Jami’an tsaro sun kashe ’yan ta’adda 8,034 a 2024
An kashe ’yan ta’adda akalla 8,034 daga cikin mutane 30,313 da dubunsu ta cika a shekarar nan ta 2024
Jami’an tsaro sun halaka ’yan ta’adda akalla 8,034 a shekarar nan ta 2024 da ke bankwana.
Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa kan Sha’anin Tsaro ya bayyana cewa wasu mutane 11,623 da ake zargi da ayyukan ta’addanci suna hannu.
Daraktan Shari’a na Ofishin, Zakari Mijinyawa, ya bayyana cewa jami’an tsaro sun yi nsasarar ceto mutane 7,967 da aka yi garkuwa da su a cikin shekarar a sassan Nijeriya.
Mijinyawa ya shaida wa ’yan jarida a ranar Litinin cewa makamai 10,200 da harsasai 224,709 ne jami’an tsaro suka kwato daga hannun ’yan ta’adda a shekarar.
- Lookman ya lashe kambun gwarzon dan kwallon Afirka na 2024
- NAJERIYA A YAU: Yadda Tamowa Ke Yaɗuwa Kamar Wutar Daji a Katsina
Ya ce jimillar mutane 30,313 ne aka kama a shekarar zargin manyan laifuka, inda aka kwato motocin sata 1,438.
Jami’an tsaro sun kuma dakile satar danyen mai kudinsa ya kai Naira biliyan 57, lamarin da ya kara yawan danyen mai da ake hakowa zuwa ganga miliyan 1.8 a kullum a Nijeriya.
Ya ce wannan nasarar ta samu ne a da hadin kan jami’an tsaro da amfani da kayan aiki na zamani da wajen aikinsu n a dakile ayyukan miyagu a yankin Neja Delta.
A cewar Mijinyawa, Hukumar Yaki da Miyagun Kwayoyi (NDLEA) ta samu gagarumar nasara wajen kama muggan kwayoyi na biliyoyin Naira tare da tsare masu safarar su da masu sha.
A bangaren Hukumar Kwastam kuma, an tara kudaden shiga Naira tiriliyan 5.49, wanda ya zarce abin da ta tara a bara da kashi 8.9%.
Hukumar kula da gandun daji kuma ta kama akalla mutane 621 tare da gurfanar da 466 daga cikinsu a kotu, baya ga wasu 61 da aka sasanta a wajen kotu.
Ya a baya ’yan ta’adda da ’yan kungiyar IPOB sun mayar da dazuka mafakarsu a dazukan Kamulu da Tafkin Chadi da Tafkin Kainji da saransu a sassan Nijeriya, wanda hakan ya haifar da barazanar tsaro.