Jami’an tsaro sun kona gidan Kwamandan IPOB
Jami’an tsaro sun banka wa gidan wani kungiyar kungiyar IPOB wuta a Jihar Imo.
Jami’an tsaro sun banka wa gidan wani kungiyar kungiyar IPOB wuta a Jihar Imo.
A safiyar Talata ne jami’an ’yan sanda a cikin motoci suka yi ta harbe-harbe, bayan sun cinna wuta a gidan da Theddus Ekechukwu (Moputu) yake zama, al’amarin da ya haifar da fargaba a zukatan mazauna.
- An yi garkuwa da mai jego an bar jaririnta
- Za a rage albashin ma’aikatan Gwamnatin Tarayya
- Juyin mulki: ‘Fadar Shugaban Kasa na cikin rudani’
- An kara sako dalibin Jami’ar Greenfield
Majiyoyi sun ce jami’an tsaron sun kai samamen ne don kama Moputu a unguwar Umuneke-Nta a karamar Hukumar Isiala Mbano ta Jihar.
Shaidu sun ce har zuwa daren ranar Litinin, Moputu mai shekara 50, wanda matarsa jami’ar ’yar sanda ce, ya yi ta gudanar da harkokinsa a unguwar.
Sun ce jami’an tsaron sun iso garin ne da misalin karfe daya na dare, inda suka yi kwanto a gidan da Moputu yake da nufin kama shi.
“Sun dade suna hakonsa da kuma bincike a gidan amma ba su gan shi a ba. Wasu sun ce tserewa ya yi, da ya ga alamar hadari.
“Da misalin karfe 8 na safe, ’yan sandan suka banka wa gidan wuta a gaban ’yan uwa da danginsa.”
Sai dai ta ce, “Gidan da kuma yawancin kayan ba na Moputu ba ne, na yayansa ne, wanda shi ne mai gidan.
“Daga nan suka yi ta harbe-harbe a iska kafin bar unguwar… Amma babu wanda aka taba.
Kakakin ’yan sanda na Jihar Imo, Orlando Ikeokwu ya ce ba shi da labari game da abin da ya faru tukuna.