Jami’an tsaro sun kwato shanun sata 1,600 a Kebbi
Akalla mutum bakwai da ake zargi da satar shanu ne jami’an tsaro na hadin gwiwar soja da ’yan sanda da ’yan sintiri suka kama a yayin wani gumurzu da suka yi a kauyukan Bena da ke karamar Hukumar Danko-Wasagu da ke Jihar Kebbi.Jami’an tsaron sun kuma yi nasarar kwato shanu 1,600 da rakuma da jakuna […]
Akalla mutum bakwai da ake zargi da satar shanu ne jami’an tsaro na hadin gwiwar soja da ’yan sanda da ’yan sintiri suka kama a yayin wani gumurzu da suka yi a kauyukan Bena da ke karamar Hukumar Danko-Wasagu da ke Jihar Kebbi.
Jami’an tsaron sun kuma yi nasarar kwato shanu 1,600 da rakuma da jakuna da awaki da tumaki masu yawa a dajin bayan gumurzun.
Mataimakin Gwamnan Jihar Kebbi, Kanar Sama’ila Dabai Yombe (mai ritaya) ne ya tabbatar wa ’yan jarida haka, inda ya ce jami’an tsaro na hadin gwiwar sun dade suna fakon barayin dabbobi tun lokacin da suka samu labarin suna cikin dajin, bayan da barayin suka dade suna addabar al’ummar yankin da satar dabbobi.
Kanar Sama’ila Yombe ya ce shanu da sauran dabbobin da aka kwato, na hannun rundunar tsaro domin ci gaba da bincike don gano masu su. Kuma ya ce ana nan ana ci gaba da bincike, domin gano sauran barayin shanun da suka gudu.
Wakilinmu ya tuntubi Shugaban kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyatti Allah ta kasa, Alhaji Mohammed Kiruwa Ardon Zuru, game da gano shanun satar, inda ya ce, jama’a da dama suna zargin Fulani da satar shanu, to amma abin ba haka yake ba, domin yanzu duk wadanda ake kamawa da satar shanu za a tarar kabilu daban-daban ne. Ya ce wadanda aka kama a yankin Bena babbansu Badakkare ne sauran Hausawa ne da Fulani.
Ya ce ba yana goyon bayan Fulani ne ba a’a duk Bafullacen da aka kama da laifin sata ko fashi a hukunta shi ko dan wane ne ko daga ina ya fito.
Sai ya yi kira ga gwamnonin Arewa su kara sa kaimi wajen yaki da barayin shanu da masu garkuwa da mutane wadanda suka addabi al’ummar yankin arewa musamman mazauna karkara.