Jami’an Tsaro Sun Kwato Wadanda Aka Sace A Kebbi

Rundunar hadin gwiwa a Jihar Kebbi ta kubutar da wasu mutane biyu da ’yan bindiga suka sace a yankin Mai Yama da ke Karamar Hukumar Suru. Jami’an tsaron da aka tura kananan hukumomin Suru da Maiyama a jihar Kebbi a ranar Talata sun ceto mutane biyu da ake zargin ’yan bindiga ne suka yi garkuwa […]

Jami’an Tsaro Sun Kwato Wadanda Aka Sace A Kebbi

Rundunar hadin gwiwa a Jihar Kebbi ta kubutar da wasu mutane biyu da ’yan bindiga suka sace a yankin Mai Yama da ke Karamar Hukumar Suru.

Jami’an tsaron da aka tura kananan hukumomin Suru da Maiyama a jihar Kebbi a ranar Talata sun ceto mutane biyu da ake zargin ’yan bindiga ne suka yi garkuwa da su a yankunan.

Rundunar ta hada da jami’an  sojin Najeriya da jami’an tsaron farin kaya da na Sibil Difens (NSCDC) da kuma kungiyoyin ’yan banga na cikin jihar.

AbdulRahman Zagga, daraktan tsaro a fadar gwamnatin da ke Birnin Kebbi ya alaƙanta nasarar da irin kokarin da Gwamna Nasir Idris ke yi na goyon bayan jami’an tsaron da kuma samar musu da kayan aikin da suke bukata.

Zagga ya ce rundunar hadin guiwar ta samu nasarar zakulo barayin daga Dajin Giro zuwa Dajin Boma kafin daga karshe su yi nasarar kubutar da mutanen a Dajin Zugu Liba.

Manoma 7 sun rasu a hatsarin mota a Minna

Farashin litar mai zai haura N1,000 kwana nan — IPMAN 

Mayaƙan Lakurawa 3 sun shiga hannu kan bayar da cin hancin N1.6m

Boko Haram ta ƙone coci da gidaje a Borno