Jami’an tsaro sun ragargaji IPOB a Ebonyi da Enugu

An kwace makamai da dama daga hannun ‘yan bindigar da suka hada bindigogi da alburusai da babura da kayan sojoji da sauransu.

Jami’an tsaro sun ragargaji IPOB a Ebonyi da Enugu

Makaman da aka kwace

Rundunar hadin gwiwar jami’an tsaro ta Operation Golden Dawn II ta kai samame a wani sansanin IPOB/ESN a kauyen Amagu da ke Karamar Hukumar Ishielu, Jihar Ebonyi.

Rahotanni sun ce jami’an tsaron sun yi dauki-ba-dadi tare da kashe wasu daga cikin mamabobin haramtacciyar kungiyar, sauran kuma suka ranta a na-kare.

A samamen na ranar Litinin, an kwace makamai da dama da suka hada da bindigogi da alburusai da babura da rigunan sojoji da sauransu.

Kazalika, jami’an tsaro sun kai makamancin samamen a wata maboyar bata-garin da ke Agubeji a Jihar Enugu inda suka cafke wani da ake zargi yana taimaka wa IPOB/ESN.

Daraktan Hulda da Jama’a na Sojoji, Brigediya-Janar Onyema Nwachukwu, ya ce wanda aka damken na ci gaba da taimaka wa jami’an tsaro wajen aikinsu a yankin.

Rundunar hadin gwiwar da ta kai samamen ta kunshi sojoji da ’yan sanda da sojojin sama da kuma jami’an DSS.