Jami’an tsaro sun ragargaji ’yan bindigar Katsina

Jami’an tsaro sun dandana wa ’yan bindigar Katsina kuda a Tsaskiya

Jami’an tsaro sun ragargaji ’yan bindigar Katsina

Hadin gwiwar ’yan sanda da sojoji sun yi nasarar dakile harin da ’yan bindiga suka kai a Tsaskiya, Karamar Hukumar Safana, Jihar Katsina.

Rundunar ’Yan Sanda ta jihar ta ce, “’Yan bindiga sama da 200 dauke da manyan bindigogi sun yi ta harbi kan mai uwa da wabi a harin da suka kai wa shingayen jami’an tsaro guda uku”.

“A yau 27/10/2020, da misalin karfe 4 na asuba, bayan samun bayanan sirri, rundunarmu da hadin gwiwar sojoji ta fatattaki ’yan bindigar da suka kai harin daukar fansa a Tsakiya, Karamar Hukumar Safana ta Jihar Katsina”, inji kakakin rundunar, SP Gambo Isah.

Sanarwar ta kara da cewa, rundunar ta yi musayar wuta da ’yan bindigar, ta kashe da dama daga cikinsu, wasu kuma suka sha da kyar da raunukan harbin bindiga.

Sai dai ya ce maharan sun kashe wani mutum mai fama da tabin hankali sannan suka yi awon gaba da wasu mata uku zuwa cikin daji.

Jami’in ya ce yanzu haka ana gudanar da bincike domin ganin an kubutar da matan daga hannun maharan.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa