Jami’an tsaro sun tsare jagoran Falasdinawa mazauna Najeriya
Jami’an tsaron Najeriya sun yi awon gaba da shugaban al’ummar Falasdinawa mazauna Najeriya a Abuja
Jami’an tsaron Najeriya sun yi awon gaba da Shugaban al’ummar Falasdinawa mazauna Najeriya, Abu Ramzi Ibrahim, a birnin Abuja
Rahotanni sun suna jami’an tsaro sun kama Abu Ramzi Ibrahim me a gidansa da ke Abuja tun ranar Juma’a.
Majiyoyi daga cikin al’ummar Falasɗinu sun ce Ibrahim, wanda dasn Bafalasɗine ne kuma ya yi karatu a jami’ar Najeriya, yana tsare har zuwa yanzu.
Wakilinmu ya yi ƙoƙarin jin ta bakin Jakadan Falasɗinu da ke Najeriya amma hakarsa ta cin ma ruwa ba.
- Rushe Kasuwar Alaba Rabo: Mun yi asarar fiye da N20bn — ’Yan Arewa
- Yau Shugabannin Tsaron Afrika 54 ke taro a Abuja
Ibrahim ya shahara wajen kare muradun Falasɗinawa ta kafafen yaɗa labarai, musamman a ’yan watannin nan da rikicin Isra’ila da Falasɗinu ke ƙara ɗaukar hankalin duniya.
Har zuwa yanzu babu wata sanarwa daga hukumomin tsaro kan batun kama shi.