Jami’an tsaro sun yi harbi a Gidan Gwamnatin Kano
Jami’an tsaron sun yi harbri bayan da masu zanga-zangar suka fara koma tayoyi a kofar shiga gidan gwamnatin
Jami’an tsaro sun yi harbe-harbe bayan masu zanga-zangar tsadar rayuwa sun yi dafifi a Babbar Kofar Gidan Gwamnatin Kano.
Jami’an tsaron sun yi harbri bayan da masu zanga-zangar suka fara koma tayoyi a kofar shiga gidan gwamnatin.
’Yan sanda sun harba hayaki mai da hawaye a yunkurinsu na watsa masu zanga-zangar tarzomar.
Masu zanga-zanga daga fadin jihar dai sun nufi gidan gwamnatin ne inda za su mika takardar kokensu.