Jami’an tsaro sun yi shiru dangane da batun jiragen yakin Tompolo

Jami’an tsaro a Legas har yanzu ba su ce komai dangane da batun jiragen ruwa na yaki da tsohon tsageran Naje-Delta, Gobernment Ekpemupolo wanda aka fi sani da Tompolo ake zargin ya saya ba. Masu magana da yawun Rundunar Sojojin Ruwa ta Yamma da Ma’aikatar Tsaro ta Tarayya ba su wani abu a kan batun […]

Jami’an tsaro sun yi shiru dangane da batun jiragen yakin Tompolo
Jami’an tsaro sun yi shiru dangane da batun jiragen yakin Tompolo

Jami’an tsaro a Legas har yanzu ba su ce komai dangane da batun jiragen ruwa na yaki da tsohon tsageran Naje-Delta, Gobernment Ekpemupolo wanda aka fi sani da Tompolo ake zargin ya saya ba.

Masu magana da yawun Rundunar Sojojin Ruwa ta Yamma da Ma’aikatar Tsaro ta Tarayya ba su wani abu a kan batun ba.
A ranar Talata Darakta-Janar din Hukumar da ke Lura da Tasoshin jiragen ruwa ta Najeriya (NIMASA) Patrick Akpobolokemi ya ce Tompolo bai sayi jiragen yaki 6. Ya ce jiragen da ake magana a kansu tuni Majalisar Tarayya ta tantance su, inda ake amfani da su wajen sintiri don kama masu fasa bututun mai da kuma fasa-kwaurinsa.
Wani babban jami’i a Rundunar Sojojin ruwa ta Yamma ya shaida wa Aminiya ba za su iya yin bayani dangane da batun jiragen da aka ce Tompolo ya saya ba, ya ce idan ma wannan batun ya zama gaskiya, to ba su da ikon cewa komai ba a kai.
Ya ce “idan har Tompolo ya sayi wadannan jirage 6 da ake fada, to Fadar Shugaban kasa ko Ma’aikatar Tsaro ta Tarayya kawai za za su tabbatar da batun ko su karyata shi.”
Ya ce tabbas kamfanin Tompolo mai suna Tompolo Global West bessels yana da sahihiyar yarjejeniyar da ya cimma da gwamnatin Tarayya don ya rika sintiri gabar tekun kasar nan don magance fasa-kwaurin man fetur.
Ya ce Tompolo yana da manyan jirage 6, kuma Hukumar NIMASA tana da masaniya a kan hakan.
“Yawancin jiragen ana amfani da su wajen sintiri a gabar tekun da ke yankin Neja-Delta.” Inji majiyar.
Aminiya ta ziyarci ofishin Kwamanda mai rike da tuta na Rundunar Sojoji ruwa ta Yamma, Alade Ilesanmi da kuma na Kwamandan da ke samar da bayanai na Rundunar Sojojin ruwa ta Yamma, Laftanar Abdussalam Sani don su yi karan haske a kan al’amarin, amma aka ce aka sun tafi don su yi jana’izar wani sojan ruwa mai suna Ajuonu.