Jami’an tsaron da suka yi wa bazawara fyade sun shiga hannu

Rundunar ’yan sanda a Jihar Jigawa ta kama wasu jami’anta bisa zarginsu da yin amfani da karfin bindiga wajan tursasa wata mata suka yi mata fyade. Matar mai suna Safiya Dingas, ’yar asalin kasar Nijar ce wadda ke zaune a karamar Hukumar Maigatari a Jihar Jigawa, Najeriya. Ta tabbatar wa Aminiya cewa a ranar Alhamis […]

Jami’an tsaron da suka yi wa bazawara fyade sun shiga hannu

Rundunar ’yan sanda a Jihar Jigawa ta kama wasu jami’anta bisa zarginsu da yin amfani da karfin bindiga wajan tursasa wata mata suka yi mata fyade.

Matar mai suna Safiya Dingas, ’yar asalin kasar Nijar ce wadda ke zaune a karamar Hukumar Maigatari a Jihar Jigawa, Najeriya. Ta tabbatar wa Aminiya cewa a ranar Alhamis ta makon jiya, ta dawo Maigatari daga Nijar, sai ta yi wa Alhaji Abba waya domin ya zo da babur ya kai ta gida. Ta ce suna cikin tafiya ne sai kawai ta ji jiwa na daukarta. Bayan sun tsaya don ta huta, kafin su ci gaba da tafiya, kawai sai ga wani jami’in dan sanda mai suna Jamilu Muhammed da kuma jami’in tsaro na farin kaya (Sibildifens) a kansu.

Ta ci gaba da cewa, jami’an tsaron sai suka tuhume ta cewa ita matar aure ce, me ya hada ta da wannan mutum da dare haka? Shi ne ta sanar da su cewa ita bazawara ce, shi kuma mai hayar babur ne zai kai ta gida.

Daga bisani dai iyayenta sun sanar da jami’an tsaron cewa Safiya bazawara ce, amma ba su amince ba sai da aka gabatar masu da takardar sakin da mijinta ya yi mata. Kan haka suka nemi da ta ba su Naira dubu goma, ita kuma ta ce ba ta da su.

Ta kara da cewa, jami’an tsaron sun ce ba za su ba ta takardarta ba sai ta biya kudin ko kuma su yi lalata da ita. Ta ce shi dan sanda Jamilu Muhammed ne ya tura ta cikin wani kango, inda shi kuma jami’in Sibildifens ya yi lalata da ita da karfin tsiya.

Kakakin rundunar ’yan sanda a Jihar Jigawa, SP Audu Jinjiri ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce jami’an biyu suna hannunsu ana kan bincike. Ya kara da cewa ya samu tabbacin cewa shi dan sandan bai aikata lalata da Safiya ba. Ya ce da zarar an kammala bincike a kansu za a gurfanar da su a gaban kotu domin a yi masu hukunci daidai da irin laifin da suka aikata.