Jami’an tsaron Dabid Mark ne suka harba wa Tambuwal barkonon tsohuwa – Jami’in ‘yan sanda

Jami’an ’yan sanda da ke tare da Shugaban Majalisar Dattijai, Dabid Mark ne suka bada wa Shugaban Majalisar Wakilai Aminu Waziri Tambuwal barkonon tsohuwa, a ranar 20 ga Nuwambar bana, a cewar babban jami’in ’yan sanda da ke farfajiyar Majalisar kasa, James Idachaba. An kulle kofa, inda wasu ’yan sanda suka mamaye majalisar, suka hana […]

Jami’an tsaron Dabid Mark ne suka harba wa Tambuwal barkonon tsohuwa – Jami’in ‘yan sanda
Jami’an tsaron Dabid Mark ne suka harba wa Tambuwal barkonon tsohuwa – Jami’in ‘yan sanda

Jami’an ’yan sanda da ke tare da Shugaban Majalisar Dattijai, Dabid Mark ne suka bada wa Shugaban Majalisar Wakilai Aminu Waziri Tambuwal barkonon tsohuwa, a ranar 20 ga Nuwambar bana, a cewar babban jami’in ’yan sanda da ke farfajiyar Majalisar kasa, James Idachaba.

An kulle kofa, inda wasu ’yan sanda suka mamaye majalisar, suka hana Tambuwal da wasu ’yan majalisa shiga cikin ginin majalisa.
Shugaban majalisar da sauran abokan aikinsa, wadanda daga bisani suka smau shiga cikin majalisar, jami’an ’yan sanda sun bada musu barkonon tsohuwa.
Majalisara Dattijai ta kafa kwamitin bincike, a karkashin jagoranci Sanata Ahmad Makarfi, dan PDP mai wakiltar Jihar Kaduna, inda aka tafka muhawara kan al’amuran da suka wakana.
Mista Idachaba, wanda ya gurfana a gaban kwmaitin ranar Litinin din da ta gabata, ya bayyana cewa, jami’an ’yan sandan Babban Birnin Tarayya ba su da hannu wajen harba barkonon tsohuwa, amma jami’an tsaron da ke tare da Shugaban Majalisar Dattijai ne ked a alhakin aikata wannanj laifin.
Sai dai kuma sauran jami’an tsaron da ke aiki a Majalisar kasa, sun ki yarda da bayanin Idachaba, shi kuwa jami’in ’yan sanda ya jajirce kan cewa ya ga bidyon da ya nuna yadda aika aikata wannan aika-aika. Sai dai bai fadi sunan wani daga cikin jami’an tsaron ba.
Ita kuwa hukumar ’yan sanda, ta bayyana cewa, ta dauki mataki ne, bisa rahoton da ta samu na cewa ’yan daba za su mamaye majalisar, a ranar da ’yan majalisar ke shirin zama don tattaunawa kan yiwuwar kara wa Shugaban kasa Goodluck Jonathan wa’adin dokar ta-baci
Idachaba ya kuma bayyana wa kwamitin cewa, kulle kofar shiga majalisar d aaka yi, ya biyo bayan umarnin d aaka bas hi daga rundunar ‘’yan sandan Babban Birnin Tarayya.
Kwmaitin ya kirawo Kwamishinan ’yan sanda na Babban Birnin Tarayya, Wilson Inalegu, tare da Daraktan Jami’an Tsaron Asiri na SSS, wadanda ake sa ran gurfanarsu a gaban kwamitin nan da wasu kwanaki, inda za su yi bayani game da mamayr da aka kai wa Majalisar kasar.