Jami’an tsaron Najeriya da Kungiyar Miyetti  Allah sun yi taro a Kebbi

Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin Muhammadu Buhari ta tura manyan shuwagabannin tsaro domin tattaunawa da shugabannin kungiyar Miyetti Allah na kasa, wanda aka gudanar a masaukin shugaban kasa dake Birnin Kebbi. Shugaban tawagar ministan ayyukan cikin gida Janar Abdulrahaman Dambazau mai ritaya, yace shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya turo su ne zuwa nan Jihar Kebbi […]

Jami’an tsaron Najeriya da Kungiyar Miyetti  Allah sun yi taro a Kebbi
Jami’an tsaron Najeriya da Kungiyar Miyetti  Allah sun yi taro a Kebbi

Gwamnatin tarayyar Najeriya karkashin jagorancin Muhammadu Buhari ta tura manyan shuwagabannin tsaro domin tattaunawa da shugabannin kungiyar Miyetti Allah na kasa, wanda aka gudanar a masaukin shugaban kasa dake Birnin Kebbi.

Shugaban tawagar ministan ayyukan cikin gida Janar Abdulrahaman Dambazau mai ritaya, yace shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya turo su ne zuwa nan Jihar Kebbi domin su tattauna da shugabannin kungiyar Miyetti Allah na Jihohi 36 harda Abuja domin samun mafita ta yadda za a kara samun kawo karshen ta’addanci da kuma satar shanu a fadin kasar nan.

Minstan yace taron da sarakunan Fulani a karkashin jagorancin shugaban kungiyar Miyetti Allah na kasa, Alhaji Muhammadu Kiruwa Ardon Zuru ya tattauna ne akan muhimman abubuwa uku da suka danganci irin goyon bayan da Fulani zasu bayar ga tsaron kasa.

Na farko: taron ya amince cewa daga yanzu sarakunan Fulani dake zaune a sassan kasarnan zasu fara aiki da shawarar shugaba Muhammadu Buhari akan batun tantance baki da ke ziyarar garuruwa da rugagensu, domin gujewa karbar bakuncin miyagun mutane masu barazana ga tsaron lafiyar Najeriya.

Na biyu:  mun tattauna ne kan irin gudunmuwar da Fulani zasu bayar ga shirin murkushe barayin shanu.

Abu na uku: shine matsalar da taki ci taki cinyewa a tsakanin manoma da makiyaya.

Da yake yiwa yan jarida bayani bayan kammala taron, mukaddishin Sufeto Janal na ‘yan sandan Najeriya, Muhammadu Adamu, yace daga yanzu sarakuna da shugabannin Fulani zasu fara aikin binciken kwakwaf ga dukkan mutumin da ya ziyarci rugarsu, domin neman zama tare dasu dan gujewa karbar miyagun mutane, masu barazana ga tsaron lafiyar kasar nan. Su kuma tabbatar da sun tona asirin duk wanda suka gani yana aikata ta’addanci, dole ne su hada kai da jami’an tsaro dan kawo karshen wannan bala’i dake damun al’ummar Najeriya musamman arewacin kasar.

Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, yace yana godiya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da ya zabi Jihar Kebbi ta dauki nauyin wannan babban taro da aka yi akan sha’anin tsaro. Yace wannan babban aiki ne kuma nauyine a wuyansu da ya kamata su tashi tsaye su wayar da kan jama’arsu game da yin kyakkyawar lura da irin mutanen da ake zaune tare dasu a cikin unguwanni da garuruwa. Irin gudumawar da ya kamata su bayar kenan ga fafitikar samar da zaman lafiya da tabbatar da tsaro da shugaba Buhari yake yi a kasar nan.

Shima da yake yiwa ‘yan jarida bayani bayan sun kammala taron, shugaban kungiyar Miyetti Allah na kasa, Alhaji Muhammadu Kiruwa, Ardon Zuru, ya ce sun yabawa shugaban kasa Muhammadu Buhari, akan yadda ya turo manyan jami’an tsaron Najeriya domin tattaunawa da sarakunan Fulani da shugabannin Miyetti Allah ,wanda ba a taba yin haka ba sai a lokacinsa. Yace sun tabbatar wa manyan jami’an tsaro dukkan bukatunsu da bada goyon baya, domin samun nasarar kawo karshen ta’addanci dake faruwa a kasar nan.

Daga cikin manyan jami’an tsaro da suka halarci taron, akwai Alhaji Yusuf Bichi, shugaban SSS da Alhaji Ahmed Rufa’i, shugaban hukumar NIA da sauran hukomomin tsaro na Najeriya.