‘Jami’an ’yan sanda 63 ’yan kungiyar Ombatse suka kashe’

Rundunar ’Yan sandan Jihar Nasarawa ta ce jami’anta 63 ne ’yan kungiyar Ombatse suka kashe a kauyen Lakyo da ke karamar Hukumar Lafiya a kwanakin baya. Rundunar ’yan sandan ta bayyana haka ne a lokacin da take gabatar da takardarta ga kwamitin binciken kisan jami’an tsaron na Mai shari’a Fola Gbadenyon a Lafiya a ranar […]

‘Jami’an ’yan sanda 63 ’yan kungiyar Ombatse suka kashe’

Umaru Tanko Al-Makura Gwamnan Jihar NasarawaRundunar ’Yan sandan Jihar Nasarawa ta ce jami’anta 63 ne ’yan kungiyar Ombatse suka kashe a kauyen Lakyo da ke karamar Hukumar Lafiya a kwanakin baya. Rundunar ’yan sandan ta bayyana haka ne a lokacin da take gabatar da takardarta ga kwamitin binciken kisan jami’an tsaron na Mai shari’a Fola Gbadenyon a Lafiya a ranar Litinin da ta gabata.
Takardar wadda Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Shehu Umaru ya rattaba wa hannu kuma Babban Sufirtandan ’Yan sanda Sam Ewa ya karanta a madadinsa an gabatar da ita ce a asirce bayan rundunar ta bukaci haka kuma shugaban kwamitin ya amince.
Sai dai wani daga cikin jami’an da suka kasance a lokacin da ake gabatar da takardar da ya bukaci a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa Majalisar Tsaro ta Jihar Nasarawa ce ta amince a tura jami’an tsaron da aka kashe a kauyen Lakyo don kama bokan Ombatse da ’yan kungiyarsa domin a hukunta su.
Bayan majalisar ta amince ne jami’an tsaro da suka hada da ’yan sanda da jami’an tsaro na farin kaya (SSS) suka tafi kauyen Lakyo don kama bokan Ombatse da rusa wurin bautarsa inda ’yan kungiyar Ombatse suka yi musu kwanton-bauna suka bude musu wuta suka kuma kone gawarwakin wasu daga cikinsu kurmus.
Kodayake a lokacin da lamarin ya auku Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya Muhammed Abubakar wanda ya ziyarci Lafiya don jajanta wa rundunar da iyalan wadanda lamarin ya shafa ya ce jami’ansa 23 ne kawai aka kashe kamar yadda shi ma Kwamishin ’Yan sandan Jihar ya sanar a lokacin, sai ga shi a lokacin gabatar da takardar rundunar ta ce an kashe ’ya’yanta 63 ne.
Jami’an tsaro sun kori manema labarai daga wurin zaman kwamitin da ake yi a Kotun Majistare ta Lafiya. Daga bisani shugaban kwamitin binciken Mai shari’a Fola Gbadeyon ya ce daga yanzu ba za a sake barin manema labarai su halarci zaman kwamitin ba.