Jami’an zabe sun yi bore a Kano
Ma’aikatan zabe sun yi barazanar kaurace wa aikin ana tsaka da rabon kayan aikin zaben shugaban kasa a safiyar Asabar
Ma’aikatan zabe sun yi bore tare da da barazanar kaurace wa aikin, a unguwar Dorayi Karama da ke Karamar Hukuma Gwale a Jihar Kano.
Ma’aikatan zabe na wucin gadi sun yi barazanar ce a lokacin da ake tsaka da rabon kayan aikin zaben shugaban kasa da ’yan Majalisar Tarayya a safiyar Asabar.
- KAI-TSAYE: Zaben Shugaban Kasar Najeriya
- Za mu fitar da sakamakon zabe a kan lokaci —INEC
- Dan takarar Gwamnan PDP ya tsallake rijiya da baya a Zamfara
Boren nasu ya samo asali ne da zargin da suke yi cewa an yi musu kwange wajen biyan su kudin alawus dinsu na samun horo.
A kan haka ne suka yi yunkurin hana ci gaba da rabon kayan aiki sannan suka jadda cewa ba za su yi aikin ba, sai an cika musu kudin alawsu dinsu.
A cewarsau, suna samun da labarin cewa N7,000 aka biya takwarorinsu a wasu jihohin, amma su N3,000 aka ba su.