Jami’ar ABU ta samar da sabbin iri masu jure yanayi

A cewarsa, Cibiyar ta gudanar da sabbin binciken irin shuka guda 108 tare da samun sakamako mai kyau.

Jami’ar ABU ta samar da sabbin iri masu jure yanayi

Cibiyar Binciken Aikin gona da ke Jami’ar Ahmadu Bello (IAR) ta samar da ingantattun irin shuka da ke jure wa yanayi mabambata domin sauwaka wa manoma hasarar amfanin gona a sakamakon sauyin yanayi.

Daraktan Cibiyar, Farfesa Muhammad Faguji Ishiyaku, ya bayyana haka a wajen taron nazarin bincike da tsare-tsare na shekara ta 2023 da ya gudana a cibiyar.

A cewarsa, Cibiyar ta gudanar da sabbin binciken irin shuka guda 108 tare da samun sakamako mai kyau.

Farfesa Muhammad Faguji Ishiyaku, ya bayyana cewa, bayan bin kwakkwafi na kwamitin sanya ido a kan sabbin iraruwa na kasa ne dukkan binciken cibiyar suka sami amincewa.

A cewarsa, jajircewar da masu buncike da sauran masana na cibiyar ne kashin bayan nasarar da ake samu.

Farfesa Faguji ya ce dukkan nasarorin da suka samu a sanadiyyar goyon baya da samar da kudi wadda Ma’aikatar Aikin Gona ta tarayya ta Santa masu da shi.

Da yake jawabi, Mataimakin Shugaban Jami’ar Ahmadu Bello, Farfesa Kabiru Bala, ya ce cibyar ta IAR ta kasance abin koyi ga sauran cibiyoyi da ke kasar nan.

Ya ce kowa na da rawar da zai taka wajen ganin Najeriya ta tsere wa tsara wajen samar da abinci.

Davido zai bai wa marayu tallafin N300m a Najeriya

Ba mu yanke hukunci kan ƙudirin harajin Tinubu ba — Abbas

Masu garkuwa da mutane na neman N10m kan manoma 6 a Taraba

Hotunan Gobarar Kasuwar Laranto da ke Jos