Jami’ar ABU za ta fara musayar ilimin aikin gona da takwararta a Ingila
Aliyu Babankarfi Zariya Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zaria ta ƙula yarjejeniya da jammi’ar Yammacin Scotland domin bunƙasa amfanin gona a nahiyar Afrika. Daraktan yaɗa labaran ABU Malam Auwal Umar ya ce an ƙulla yarjejeniyar ne ƙarƙashin shirin Musayar Ilimin Noma na Nahiyar Afirka. An koma karatu a Jami’ar Ahmadu Bello Jami’ar Ahmadu Bello ta kirkiro […]
Aliyu Babankarfi Zariya
Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zaria ta ƙula yarjejeniya da jammi’ar Yammacin Scotland domin bunƙasa amfanin gona a nahiyar Afrika.
Daraktan yaɗa labaran ABU Malam Auwal Umar ya ce an ƙulla yarjejeniyar ne ƙarƙashin shirin Musayar Ilimin Noma na Nahiyar Afirka.
An koma karatu a Jami’ar Ahmadu Bello
Jami’ar Ahmadu Bello ta kirkiro sabon takin zamani don bunkasa noma
Yace ƙawancen zai taimaka wurin musanyar ilimi kan dabarun bunƙasa ribar ƙananan manoma da kamfanonin sarrafa amfanin gona a ƙasashen Nigeria, Ghana, Kenya da Afirka ta Kudu.
Malam Auwal Umar yace Ƙungiyar ƴan Afirka mazauna Scotland ce ta taimaka wurin ƙulla alaƙa tsakanin jami’o’in biyu.