Jami’ar ABU Zariya za ta amfana da ayyukan Naira miliyan 800

Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya za ta amfana da ayyuka na kimanin Naira miliyan 800 daga sashin kula da yanayin zaizayar kasa da ke ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya. Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Boss Gado Mustapha ne ya bayyana haka a wajen taron da kungiyar Tsofaffin daliban Jami’ar Ahmadu Bello ta gudanar a Zariya, inda […]

Jami’ar ABU Zariya za ta amfana da ayyukan Naira miliyan 800
Jami’ar ABU Zariya za ta amfana da ayyukan Naira miliyan 800

Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya za ta amfana da ayyuka na kimanin Naira miliyan 800 daga sashin kula da yanayin zaizayar kasa da ke ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya.

Sakataren Gwamnatin Tarayya, Mista Boss Gado Mustapha ne ya bayyana haka a wajen taron da kungiyar Tsofaffin daliban Jami’ar Ahmadu Bello ta gudanar a Zariya, inda ya kasance Babban Bako.

Ya ce tuni suka dauki muhimmin aiki guda daya da za su gudanar a Jami’ar Ahmadu Bello a matsayin godiya bisa ilimin da suka samu a lokacin da suke dalibanta.

A cewarsa, irin wannan gudunmawa ga jami’a za ta taimaka wajen bunkasawa da ci gaban ilimi a Najeriya tare da samar da ingantattun dalibai a karshen karatunsu.

Sakataren Gwamnatin Tarayyar ya bayyana gamsuwa tare da jin dadin kan matsayin Jami’ar Ahmadu Bello take ciki,  inda ya ce ta darar wa tsara a wannan nahiya ta Afirka. Ya ce nasarorin da ake samu sun  samu ne sakamakon tsayin-daka da sanin ya kamata da tsofaffin daliban jami’ar ke nunawa domin ci gabanta, musamman yadda take samar da hazikan jami’an gwamnati da na bangarorin masu zaman kansu.

Boss Mustapha ya yaba wa tsofaffin daliban bisa yadda suke jajarcewa don ganin sun taru duk shekara, ba tare da wani tsaiko ba. Haka kuma ya jinjina wa Shugaban Gudanarwar Jami’ar, Malam Adamu Fika wanda ya ce uba ne ga duk wani dan bokon Arewa, musamman a fagen gudanar da mulki.