Jami’ar Ahmadu Bello ta samu nasarar bunkasa irin shuka a bana
Shugaban Cibiyar Binciken Aikin Gona ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Muhammad Ishiaku ya ce, duk da matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka na tsuke bakin aljihunta wajen gudanar bincike a fannin aikin gona, cibiyar ta yi namijin kokari wajen bunkasa sababbin iri da za su samar da amfani mai yawa a bana. […]
Shugaban Cibiyar Binciken Aikin Gona ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Farfesa Muhammad Ishiaku ya ce, duk da matakin da Gwamnatin Tarayya ta dauka na tsuke bakin aljihunta wajen gudanar bincike a fannin aikin gona, cibiyar ta yi namijin kokari wajen bunkasa sababbin iri da za su samar da amfani mai yawa a bana.
Shugaban ya bayyana haka ne wajen taron kara wa juna sani na shekara-shekara don bunkasa samar da iri mai taken “Wanne ne ya fi Muhimmanci ga Manomi Tsakanin Saukin Kayan Aiki da Darajar Amfanin Gona?” wanda ya gudana a dakin taron cibiyar da ke Samaru, Zariya.
Farfesa Muhammad Ishiaku ya ce, makasudin taron kara wa juna sanin shi ne, a samar da wani yanayi da masu ilimin kimiyya da masu gudanar da tsare-tsare za su hadu da manoma domin bayyana musu irin ci gaban da aka samu wanda zai taimaka wajen bunkasa aikin gona a kowace shekara.
Saboda haka ne ma ya ce, a bana cibiyar ta samu nasarar bunkasa wasu sababbin iri na dawa guda biyu, masu suna “CSR-H 04” da “CSR- H 03” da na masara masu suna “Sammaz 41” da “Sammaz 42.”
Ya ce baya ga wadannan cibiyar ta samu nasarar bunkasa irin gyada nau’o’i 26 da na auduga guda 13 da na wake 14 da na dawa 41 da kuma na masara 42.
Ta fuskar bunkasa kayan noman zamani, shugaban yac e ba a bar cibiyar a baya ba, domin ta samar da babbar na’ura ta sheke dawa da gero da waken soya mai yawan gaske cikn dan karamin lokaci.
Tun farko a jawabin Shugaban Jami’ar Farfesa Abdullahi Mustafa ya yaba wa cibiyar bisa nasarar da take samu ta bunkasa harkar noma a wannan kasa. Sannan ya yi alkawarin ci gaba da ba ta cikakken goyon baya wajen ganin cewa wannan nasara ta ci gaba da tabbata.