… Jami’ar Al-Azhar ta ce ayyukan Boko Haram sun saba wa Musulunci
Fitacciyar Jami’ar nan ta Musulunci da ke kasar Masar da aka fi sani da Jami’ar Al-Azhar ta fitar da wata fatawa da ke cewa ayyukan kungiyar Jama’atu Ahlis Sunnah Lid Da’awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram sun saba wa koyarwar addinnin Musulunci.Jami’ar Al-Azhar, wacce ke bin Mazhabin Sunni, ta kuma bukaci […]
Fitacciyar Jami’ar nan ta Musulunci da ke kasar Masar da aka fi sani da Jami’ar Al-Azhar ta fitar da wata fatawa da ke cewa ayyukan kungiyar Jama’atu Ahlis Sunnah Lid Da’awati Wal Jihad da aka fi sani da Boko Haram sun saba wa koyarwar addinnin Musulunci.
Jami’ar Al-Azhar, wacce ke bin Mazhabin Sunni, ta kuma bukaci ’ya’yan kungiyar Boko Haram din su sako ’yan matan da suka sace ba tare da bata lokaci ba.
A ranar 14 ga watan Afrilu da ya gabata ne aka sace wasu dailbai ’yan mata su 276 a wata makarantar sakandare da ke garin Chibok a Jihar Borno, kuma bayan fiye da mako biyu sai shugaban kungiyar ta Boko Haram Abubakar Shekau ya ce kungiyarsa ce ta sace ’yan matan 276.
Wasu daga cikin ’yan matan sun kubuce a yayin da fiye da 200 ke hannun ’yan Boko Haram din.
A sassa da dama na kasar nan, ana ci gaba da nuna kaduwa da kuma takaici kan faifan bidiyon da kungiyar Boko Haram ta fitar a ranar Litinin da ta gabata.
Abubakar Shekau a bidiyon ya ce kungiyarsu ce ta sace daliban, mako uku da suka wuce, ya kuma ce suna da niyyar sayar da su.