Jami’ar Amurka ta ba daliban Jami’ar Adamawa aron ajin karatu
Sakamakon hare-haren Boko Haram da ke barazana ga daliban Jami’ar Jihar Adamawa (ADSU) da ke Mubi, Jami’ar Amurka a Najeriya (AUN) ta ba daliba 138 da suke ajin karshe ta jami’ar jihar aron ajin karatu na mako shida. Shugaban Jami’ar Amurka a Najeriya, Dokta Margee Ensign ta bayyana haka ga manema labarai a ofishinta da […]
Sakamakon hare-haren Boko Haram da ke barazana ga daliban Jami’ar Jihar Adamawa (ADSU) da ke Mubi, Jami’ar Amurka a Najeriya (AUN) ta ba daliba 138 da suke ajin karshe ta jami’ar jihar aron ajin karatu na mako shida. Shugaban Jami’ar Amurka a Najeriya, Dokta Margee Ensign ta bayyana haka ga manema labarai a ofishinta da ke Yola. Ta ce “Jami’armu ta samu ci gaba da karbuwa don haka ne ya sa muka damu da daliban da ke wasu jami’o’in. Mu na son kowane dalibi ya cika burinsa na son zama abin da ya yi niyya a nan gaba.” Dokta Emsign ta kara da cewa “Shugaban Jami’ar Jihar Adamawa ya nemi mu taimaka wa daliban Physics da Chemistry da Biology domin su rubuta jarrabawarsu a jami’armu Mun ba su mako shida domin su yi amfani da na’urorin ajin domin su koyi karatu kuma su rubuta jarrabawa.” Shugaban ADSU, Farfesa Dabid Joshua ya ba daliban shawarar su yi amfani da damar da suka samu. Ya ce, “Jami’ar AUN ta ba su dama ce da za ta taimaka wa rayuwarsu don gama karatun digirgir na wannan karon. Jami’ar ta ba mu aji mai suna Peter Okocha domin kammala jarrabawa.” Shugaban ADSU ya ce Jami’ar AUN ta taba bada irin wannan dama ga daliban neman gurbin shiga jami’a (IJMB) domin rubuta jarrabawarsu. Idan ba a manta ba dalibai da malaman ADSU sun bar jami’ar sakamakon hare-haren ‘yan Boko Haram a ranar 29 ga Oktoban 2014, inda aka kone wasu kayan aikin makarantar da gidaje.