Jami’ar AUN ta ba ’yan matan Chibok 4 guraben karatu

A ranar Litinin da ta gabata ce Jami’ar Amurka a Najeriya (AUN) ta debi sababbin dalibai 196 wadanda hudu ’yan matan Chibok ne da aka ceto. Sababbin daliban sun hade da wadanda za su yi karatun digiri da masu neman digiri na biyu da kuma wadanda za su yi karatun diploma. Shugabar Jami’ar, Dawn Dekkle […]

Jami’ar AUN ta ba ’yan matan Chibok 4 guraben karatu
Jami’ar AUN ta ba ’yan matan Chibok 4 guraben karatu

A ranar Litinin da ta gabata ce Jami’ar Amurka a Najeriya (AUN) ta debi sababbin dalibai 196 wadanda hudu ’yan matan Chibok ne da aka ceto.

Sababbin daliban sun hade da wadanda za su yi karatun digiri da masu neman digiri na biyu da kuma wadanda za su yi karatun diploma.

Shugabar Jami’ar, Dawn Dekkle ta dauki alkawarin bai wa daliban kariya a lokacin zamansu domin karatu a jami’ar.

“Ina mai mika godiyata ga iyayen wadannan sababbin daliban na Jami’ar AUN. Kada ku yi shakka ko kokwanton barin ’ya’yanku a wajenmu. Mu ma za mu yi iya namu kokarin domin ganin cewa mun bai wa daliban kyakkyawan tsaro da kulawa,” inji ta.

“Za mu yi iya kokarinmu domin ganin mun ba su ilimi, wanda zai amfane su ta yadda wata rana za su mamaye manyan kujerun mulkin kasar nan,” inji Shugabar Jami’ar.

Shugabar ta kara da cewa, a cikin sababbin daliban akwai hudu wadanda ’yan matan Chibok ne da aka sanya domin tallafa musu wajen ba su ilimi mai amfani.

Shi kuwa Mataimakin Shugabar Jami’ar, Mista Byron Bullock a nasa bangaren, gargadi ya yi ga sababbin daliban su kula kansu a yayin da suke cikin makarantar, cewa su guji yin alaka da abokan banza.