Jami’ar dan Fodiyo ta yaye likitoci 52

Jami’ar Usman dan Fodiyo da ke Sakkwato ta yaye likitoci 52 a wani bikin da aka gudanar a babban dakin taro na jami’ar a ranar Talatar makon jiya. A jawabin Shugaban Jami’ar Farfesa Abdullahi Abdu Zuru ya shawarci likitocin da aka yaye su dauki nasarar da suka samu a matsayin ta al’umma gaba daya, don […]

Jami’ar dan Fodiyo ta yaye likitoci 52
Jami’ar dan Fodiyo ta yaye likitoci 52

Jami’ar Usman dan Fodiyo da ke Sakkwato ta yaye likitoci 52 a wani bikin da aka gudanar a babban dakin taro na jami’ar a ranar Talatar makon jiya.

A jawabin Shugaban Jami’ar Farfesa Abdullahi Abdu Zuru ya shawarci likitocin da aka yaye su dauki nasarar da suka samu a matsayin ta al’umma gaba daya, don haka su mayar da hankali wajen ceto rayukan al’umma maimakon bukatun kansu kadai.
Ya ce, “Wannan takardar digiri da kuke gani ta dindindin ce, kuma ta wucin gadi ce a lokaci guda, saboda da zarar mutum ya saba wa dokar aikin likita, ya je ya rika yin yadda ya ga dama yana cin zarafin al’umma muka samu labara, to, za mu janye takardar shaidar da muka ba shi, don haka muna kira ga sababbin likitocinmu na shekarar karatu ta 2012/2013, su yi aiki tukuru wajen taimakon jama’a da ilimin da suka samu kuma jami’a za ta yi alfahari da su duk inda suka shiga matukar suka ci gaba da nuna hali nagari.”
Farfesa Abdullahi Zuru ya gode wa gwamnatocin jihohin Sakkwato da Kebbi da Zamfara kan gudunmuwar da suke ba su a koyaushe, bayan gudunmawar Naira miliyan uku da suke badawa don kula da harkokin makarantar. Tun daga farko Shugaban Tsangayar Ilimin Likitanci na Jami’ar, Farfesa Mungadi ya ce yayewar ita ce karo ta 26 da suka yi kuma suna samun nasara daidai gwargwado. Farfesa Mugandi ya ce, sun yarda da kwarewa da gogewar daliban 52 a matsayinsu na likitoci a fanni daban-daban, inda ya yi fatar za su bi sahun ’yan uwansu da suka gabata, wadanda ta sanya ana aiko wa jami’ar da takardar neman a tura su aiki a kasashen waje irin su Kanada da sauransu.
Shugaban kungiyar Likitoci ta kasa reshen Jihar Sakkwato ya yi maraba da sababbin likitocin tare da yi musu alkawarin tafya da su yanda ya kamata, kuma kungiyar ta tallafa wa kowanensu da Naira dubu 20 a matsayin kudin sufuri zuwa gida.