Jami’ar Gombe ta kaddamar da tsarin hana cin zarafin jima’i

Jami’ar Jihar Gombe ta kaddamar da sabon Tsarin Hana Cin Zarafin Jima’i domin kare ɗalibai da ma’aikata tare da tabbatar da adalci da bin ƙa’ida a harkokin ilimi.

Jami’ar Gombe ta kaddamar da tsarin hana cin zarafin jima’i

Jami’ar Jihar Gombe ta kaddamar da sabon Tsarin Hana Cin Zarafin Jima’i domin kare ɗalibai da ma’aikata tare da tabbatar da adalci da bin ƙa’ida a harkokin ilimi.

An bayyana tsarin ne a wani taro da ya haɗa shugabannin jami’a, ƙungiyoyin fararen hula, masu fafutukar kare haƙƙin mata da wakilan hukumomin gwamnati, inda aka nuna damuwa kan yawaitar irin waɗannan matsaloli a manyan makarantu.

Daraktar Cibiyar Nazarin Harkokin Jinsi ta jami’ar, Farfesa Aishatu Abubakar Kumo, ta ce tsarin ya tanadi hanyoyin zamani wajen gano laifi, karɓar ƙorafi da kuma hukunta duk wanda aka samu da laifi. 

Ta bayyana cewa cin zarafin jima’i a ƙarƙashin tsarin ya haɗa da kalamai marasa dacewa, taɓawa, ishara ko saƙonnin waya da ke tauye mutunci, tana mai jaddada cewa jami’ar ba za ta lamunci duk wani abu da zai lalata ingancin ilimi ko tsaro ba.

“Nasara a ilimi dole ta kasance bisa cancanta, ba tare da amfani da iko ko matsayi wajen cin gajiyar wani ba,” in ji ta.

Farfesa Kumo ta ƙara da cewa tsarin zai ƙarfafa ɗa’a da kyakkyawar mu’amala tsakanin malamai da ɗalibai, tare da tabbatar da gaskiya da mutunta juna a dukkan fannoni na jami’ar. Sabon tsarin ya kuma tanadi hanyoyin kai ƙara cikin sirri, domin bai wa waɗanda abin ya shafa ko shaidu damar bayyana gaskiya ba tare da tsoron tsangwama ko ramuwar gayya ba.

An kafa kwamitin bincike mai zaman kansa da zai riqa duba ƙorafe-ƙorafe tare da ba da shawarar hukunci bisa adalci. Sai dai jami’ar ta yi gargaɗi kan ƙorafe-ƙorafen bogi, tana mai cewa za a binciki kowane rahoto dalla-dalla.

A nata ɓangaren, wakiliyar ƙungiyar Gender Mobile Initiative, Fatima Abdullahi, ta yaba wa jami’ar bisa wannan shiri, tana mai cewa babban ci gaba ne wajen tabbatar da tsaro da gaskiya a makarantu. Ta bayyana cewa tsarin ya ƙunshi ingantattun hanyoyin kai ƙara, kariyar sirri, tallafa wa waɗanda abin ya shafa, da kuma hukunci mai tsauri ga masu laifi.

Hakazalika, ta gabatar da wata manhaja mai suna Campus Pal App, wadda za ta taimaka wa ɗalibai su kai rahoto cikin sauƙi da samun taimako cikin gaggawa.

Wakilai daga Ma’aikatar Shari’a, NAPTIP da NSCDC sun yaba wa wannan mataki, suna masu cewa lokaci ya yi da za a ɗauki irin waɗannan tsare-tsare domin magance matsalar gaba ɗaya.

Masu ruwa da tsaki sun kuma bukaci a ƙara wayar da kai, ƙarfafa tsarin kai ƙara, tare da tabbatar da hukunta masu laifi ba tare da nuna son kai ba.

An rufe taron da sabunta alƙawarin haɗin gwiwa daga dukkan ɓangarori domin ganin an aiwatar da tsarin yadda ya kamata, tare da gina jami’a mai tsaro, mutunci da bin doka.