Jami’ar Gombe ta sanya CCTV don inganta tsaro
Mahukuntan jami’ar sun ɗauki matakin ne domin inganta tsaron ɗalibai da ma’aikata.
Jami’ar Jihar Gombe (GSU), ta fara sanya kyamarorin CCTV a wurare daban-daban na harabar makarantar domin inganta tsaron ɗalibai da ma’aikata
Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Sani Yauta ne, ya bayyana hakan yayin taron Kwamitin Hulɗa da Al’umma na jami’ar.
- Zaben cike gurbi: Matsalar BVAS ta hana masu zaɓe jefa ƙuri’a a Ondo
- Iran ta sake rufe Mashigin Hormuz saboda Hare-Haren Isra’ila a Lebanon
Ya ce jami’ar ta ɗauki wannan mataki ne bayan fuskantar wasu matsalolin tsaro a baya-bayan nan, musamman satar babura da aka riƙa yi a cikin harabar makarantar.
A cewarsa, jami’ar ta kama wani mutum da ake zargi da satar babura guda biyar, abin da ya nuna muhimmancin ƙara tsaurara matakan tsaro.
Farfesa Yauta, ya ce baya ga sanya kyamarorin CCTV, jami’ar ta kuma fara amfani da jirage marasa matuƙa wajen sintiri da sanya ido, musamman da daddare, domin hana aikata laifuka da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar makarantar.
Dangane da shiga jami’a kuwa, ya bayyana cewa an amince da maki 150 a matsayin mafi ƙarancin makin shiga jami’ar, yayin da masu neman gurbin karatu a fannin Shari’a da Likitanci za su nemi maki 200 zuwa sama.
Haka kuma, ya shawarci iyaye da su karɓi duk wata damar karatu da aka bai wa ’ya’yansu, yana mai jaddada cewa kowane fanni na ilimi na da muhimmanci wajen bunƙasa rayuwar mutum.
Sai dai ya nuna damuwa kan yadda dabbobi ke shiga harabar jami’ar suna lalata tsirrai da wuraren da aka ƙawata.
Saboda haka ya roƙi mambobin kwamitin da su taimaka wajen magance matsalar.
A nata jawabin, jami’ar a Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi (NDLEA), Misis Orpha Gabriel, ta ba da shawarar fara yi wa ɗalibai gwajin miyagun ƙwayoyi a cikin jami’ar.