Jami’ar Jigawa za ta fara karatu a watan gobe –Farfesa Wakili

Jami’ar Jihar Jigawa za ta fara aiki da kwasa-kwasai 15 da tsangayar karatu uku a watan gobe.Kwamashinan Ilimi na Jihar Jigawa Farfesa Haruna Wakili ne ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci sabon shugaban jami’ar Farfesa Abdullahi Yusuf Ribadu zuwa fadar gwamnatin jihar tare da sauran malamai tara da gwamnatin jihar ta tsamo su daga […]

Jami’ar Jigawa za ta fara karatu a watan gobe –Farfesa Wakili

Jami’ar Jihar Jigawa za ta fara aiki da kwasa-kwasai 15 da tsangayar karatu uku a watan gobe.
Kwamashinan Ilimi na Jihar Jigawa Farfesa Haruna Wakili ne ya bayyana haka lokacin da ya jagoranci sabon shugaban jami’ar Farfesa Abdullahi Yusuf Ribadu zuwa fadar gwamnatin jihar tare da sauran malamai tara da gwamnatin jihar ta tsamo su daga manyan jami’o’in kasar nan don jami’ar ta samu tsayawa da kafarta.
Farfesa Wakili ya ce sabuwar jami’ar jihar za ta gogayya da jami’o’in jihohi 29 da sauran na tarayya don zama zakara a tsakaninsu saboda tanadin da aka yi mata.
Ya ce gwamnatin jihar ta dauki matakan kafa jami’ar ce saboda karancin guraben karatu da ’yan asalin jihar suke fuskanta a makarantun kasar nan, inda ya ce za a dauki dalibai 8,500 a karon farko a jami’ar.
Mafiya yawann malaman an dauko su ne daga Jami’ar Bayero da ke Kano da makarantar FCE.
Da yake bayani Gwamnan Jihar Jigawa Alhaji Sule Lamido ya gode wa shugabannin jami’ar da amince su yi wa jihar aiki domin agaza mata ta fannin habaka ilimi. Ya ce duk abin da wata jiha za ta yi tunkaho ko da shi akwai a Jihar Jigawa.
Ya hore su da su rike amana, inda ya ce matsalar kasar nan rashin iya jagoranci na shugabanni ne da suke danne hakkin na kasa saboda biyan bukatunsu na kashin kai.
A jawabin Farfesa Abdullahi Ribadu ya ce za su rike amana kamar yadda Gwamnan ya ba su, kuma za su yi iyakacin iyawarsu wajen tabbatar da adalci da aiki da gaskiya don ganin makarantar ta tsaya da kafafunta.