Jami’ar Jihar Gombe za ta fara sabbin darussa 6 a fannin noma

Za a gudanar da shirye-shiryen ne a sabuwar Tsangayar Noma da aka kafa a garin Malam Sidi da ke Karamar Hukumar Kwami.

Jami’ar Jihar Gombe za ta fara sabbin darussa 6 a fannin noma

Hukumar Kula da Jami’o’i ta Kasa (NUC) ta amince da fara karɓar dalibai a sabbin darussa guda shida a fannin noma a Jami’ar Jihar Gombe (GSU) a shekarar karatun 2025/2026.

Za a gudanar da shirye-shiryen ne a sabuwar Tsangayar Noma da aka kafa a garin Malam Sidi da ke Karamar Hukumar Kwami.

A ranar Litinin bayan taron majalisar gudanarwar jihar, Kwamishinan Noma da Kiwo, Barnabas Malle, ya bayyana cewa an amince da fara aikin sabuwar tsangayar aikin nomar ce ranar 21 ga Watan Mayu, 2025.

Sabbin darussan da aka amince da su sun haɗa da digir a bangaren Noma, Digiri a bangaren Gandun Daji da Dabbobin Jeji, Digiri a Kimiyyar Noma da Digiri a Kimiyyar Kasa, sai Digiri a fannin Tattalin Arzikin Noma.

Barnabas Malle ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ware filin gona mai girman hektar 365 a Garin Tafida da ke Karamar Hukumar Yamaltu Deba, domin bincike da aikin gwaji na ɗalibai.

Ya kara da cewa ana kokarin samun ƙarin fili a Garin Kurugu da ke Karamar Hukumar Kwami, don fadada ayyukan kwalejin a nan gaba.

Kwamishinan Ilimi Mai zurfi, Shettima Gadam, ya kuma tabbatar da cewa NUC ta ba da cikakken izini ga jami’ar don fara daukar daliban ne a wadannan darussa daga shekarar karatun 2025/2026.