Jami’ar Jihar Sakkwato za ta fara karatu Litinin mai zuwa
Sabuwar Jami’ar Jihar Sakkwato da ake kan gina ta za ta fara karatu a ranar Litinin mai zuwa, kamar yadda Shugaban Jami’ar Farfesa Nuhu Yakub ya shaida wa manema labarai a ofishinsa da ke mazaunin jami’ar na dindindin.Farfesa Nuhu ya ce za su samar da sahihiyar ci gaba a fannin ilimi da zai kawo alfanu […]
Sabuwar Jami’ar Jihar Sakkwato da ake kan gina ta za ta fara karatu a ranar Litinin mai zuwa, kamar yadda Shugaban Jami’ar Farfesa Nuhu Yakub ya shaida wa manema labarai a ofishinsa da ke mazaunin jami’ar na dindindin.
Farfesa Nuhu ya ce za su samar da sahihiyar ci gaba a fannin ilimi da zai kawo alfanu ga jihar
“Za mu tsaya kan ingantaccen tsari don tabbatar da samun kwararrun dalibai da za mu rika yayewa,” inji Farfesan.
Da ya juwa kan malaman da suka dauka ya ce ba ya da shakku kan kwarewarsu, ya ce sun dauki malamai 120 har da mutanen kasashen waje 18 , 12 daga Indiya, 3 sun fito ne daga Pakistan da Masar, kuma dukkansu za su kula da tsangayoyin makarantar. “Kuma duk shirye-shiryenmu sun kammala don samun nasara.”
Ya ce ana sa ran Hukumar Kula da Jami’o’i ta kasa za ta turo jami’anta a ranar Litinin mai zuwa lokacin soma zangon farko na makarantar, daga nan ba za su kara dawowa ba sai bayan shekara uku don ganin yanayin ingancin kwasa-kwasan da suke gabaarwa.
Da farko Magatakar Jami’ar Hajiya Amina Garba ta ce jami’ar za ta soma karatu ne da dalibai 100 da za su karanci sassa daban-daban, kuma a bukaci daliban su yi taka tsan-tsan da ka’idojin makarantar.