Jamiar Otuoke ta kwace mukaman farfesa 7 bisa saba ka’ida

Hukumar Gudanarwar Jami’ar Tarayya da ke Otuoke a Jihar Bayelsa ta kwace mukaman wadansu farfesoshi su bakwai ta hanyar rage musu daraja a farkon wannan mako. A takardar sanarwa da ya fitar wacce Aminiya ta samu kwafi, Magatakardar Jami’ar, Mista Iruo Yousuo ta ce Hukumar Gudanarwar Jami’ar ce ta dauki matakin a kan shehunan malaman […]

Jamiar Otuoke ta kwace mukaman farfesa 7 bisa saba ka’ida
Jamiar Otuoke ta kwace mukaman farfesa 7 bisa saba ka’ida

Hukumar Gudanarwar Jami’ar Tarayya da ke Otuoke a Jihar Bayelsa ta kwace mukaman wadansu farfesoshi su bakwai ta hanyar rage musu daraja a farkon wannan mako.

A takardar sanarwa da ya fitar wacce Aminiya ta samu kwafi, Magatakardar Jami’ar, Mista Iruo Yousuo ta ce Hukumar Gudanarwar Jami’ar ce ta dauki matakin a kan shehunan malaman jami’ar,  yayin taronta karo na 10, inda aka rage musu matsayi sakamakon abin da ta bayyana sakaci da kuma rashin kwazo.

Malaman da matsalar ta shafa sun hada da Dokta Stebe Nwabuzor wanda aka rage wa matsayi zuwa lakcara na I da Dokta Leonard Shilgba daga matsayin Farfesa babban laccara. Sauran su ne Dokta Timothy Falade Obalade daga matsayin mai neman Farfesa zuwa matakin babban laccara, sai kuma Dokta Felina Nwadike, daga matsayin mai neman zama Farfesa zuwa babban laccara.

Yayin da aka mai da Dokta Sepibo Lawson Jack zuwa karamin lakcara daga mai neman zama Farfesa. Sai kuma Dokta Marcellina Offoha da Dokta Ebans Eze, daga matsayin masu neman zama Farfesa zuwa matakan kananan laccara na daya da na biyu.

Haka kuma sanarwar ta bayyana malamai uku da suka hada da Obalade da Nwadike da kuma Lawson Jack an mayar da aikin karantarwarsu matsayin na kwantaragi.

Kuma ta sanar da samun wadansu daga cikin ma’aikatan jami’ar da barin wurin aikinsu ba bisa ka’ida ba. Ma’aikatan da ake zargi inji hukumar jami’ar, su ne Mista Obele Gabriel da Modozie Rejoice Chineye da Mista Akpan Ufot da Mista Bomor Tarela da Mista Anthony Arhogor da kuma Bassey Affiong Agbor.

Shugaban Kungiyar Malaman  Jami’o’i ta Jami’ar, Dokta Joseph Omoro ya yaba da matakin da Hukumar Gudanarwar Jam’ar ta dauka na rage matsayin malaman, yana mai cewa abin a yaba ne.