Jami’ar Tarayya ta Gashuwa ta rantsar da sababbin dalibai

Jami’ar Tarayya da ke garin Gashuwa a Jihar Yobe ta rantsar da sababbin dalibanta kimanin 244 da za su yi karatu a tsangayoyi daban-daban a shekarar karatu ta bana.Da yake jawabin ya yin rantsar da daliban Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Gaidam wanda Mataimakinsa Injiniya Abubakar D. Ali ya wakilta ya ce gwamnatinsu na aiki tukuru […]

Jami’ar Tarayya ta Gashuwa ta rantsar da sababbin dalibai
Jami’ar Tarayya ta Gashuwa ta rantsar da sababbin dalibai

Jami’ar Tarayya da ke garin Gashuwa a Jihar Yobe ta rantsar da sababbin dalibanta kimanin 244 da za su yi karatu a tsangayoyi daban-daban a shekarar karatu ta bana.
Da yake jawabin ya yin rantsar da daliban Gwamnan Jihar Alhaji Ibrahim Gaidam wanda Mataimakinsa Injiniya Abubakar D. Ali ya wakilta ya ce gwamnatinsu na aiki tukuru don ciyar da harkokin ilimi gaba.
Gwamnan ya kara da cewa gwamnatinsa tuni ta dukufa wajen samar da yanayi mai inganci a manyan makarantun jihar ciki har da na Gwamnatin Tarayya musamman ta wajen gine-gine da makamantansu.
Ya yi fata sababbin daliban da aka rantsar za su bi dokokin makarantar tare da yin abubuwan da suka kawo su a matsayinsu na shugabannin gobe.
Tun farko da yake jawabi Shugaban Jami’ar Farfesa Shehu Abdulrahman ya yaba wa gwamnatin jihar ne dangane da yadda take tallafa musu duk da cewar jami’ar mallakar Gwamnatin Tarayya ce.
Daga nan sai ya gargadi sababbin daliban su zama mutane nagari kuma su kauce wa shaye-shaye da satar jarrabawa.
Magatakardar Jami’ar Dokta Sule Dauda ne ya kaddamar da daliban, inda ya ce dalibai 130 za su yi karatu ne a fannin ilimin kimiyya, yayin da 114 za su yi karatu a wasu sauran bangarorin ilimi da jami’ar ke da su a yanzu.