Jami’ar Usmanu Danfodiyo za ta fara dashen koda
Da yake karin haske kan batun, Mungandi ya ce, “Muna da dukkan kayan aikin da ake bukata don aiwatar da dashen koda.
Za a fara aikin dashen koda a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Usmanu Danfodiyo ta Sakkwato (UDUTH), A shekara mai kamawa idan Allah Ya kai mu.
Daraktan cibiyar nazarin lafiyar mafitsara da koda na jami’ar, Farfesa Isma’ila Mungandi ne ya bayyana hakan ranar Laraba.
- Rikicin siyasa ya ci rayuka 1,525 a Najeriya —Rahoto
- NAJERIYA A YAU: Matsayin Kuri’ar ’Yan Gudun Hijira A Zaben 2023
Da yake karin haske kan batun, Mungandi ya ce, “Muna da dukkan kayan aikin da ake bukata don aiwatar da tiyatar dashen koda.
“Za mu hada hannu ne da Cibiyar Nazarin Lafiyar Mafitsara da Koda ta Jami’ar Mansoura da ke kasar Masar.
“Mun riga mun rattaba hannu a Yarjejeniyar Fahimtar Juna” don cimma wannan kuduri in ji shi.
(NAN)