Jami’in da ya lura da wasan Kano Pillars da Ikorodu United ya mutu a Otel

Tanko Nuru jami’in da ya lura da yadda wasa ya kaya a tsakanin Kano Pillars da Ikorodu United (Match Commissioner) ya rasu.  An tsinci gawarsa ce a Otel din da ya sauka a Kano.dan asalin Jihar Nasarawa, an ce ba a san dalilin rasuwar tasa ba.    Jim kadan bayan an kammala kwallo a tsakanin Pillars […]

Jami’in da ya lura da wasan Kano Pillars da Ikorodu United ya mutu a Otel
Jami’in da ya lura da wasan Kano Pillars da Ikorodu United ya mutu a Otel

Tanko Nuru jami’in da ya lura da yadda wasa ya kaya a tsakanin Kano Pillars da Ikorodu United (Match Commissioner) ya rasu.  An tsinci gawarsa ce a Otel din da ya sauka a Kano.
dan asalin Jihar Nasarawa, an ce ba a san dalilin rasuwar tasa ba.    Jim kadan bayan an kammala kwallo a tsakanin Pillars da Ikorodu United wanda ya kasance jami’in da ya lura da yadda wasan ya kaya ne (Match Comissioner) sai ya nufi masaukinsa a wani Otel da ba a ambata ba, inda a washegari ne aka tsinci gawarsa.  Labarin rasuwar tasa ya bazu ne bayan kulob din Ikorodu United ya watsa a shafin sadarwarsa na Twitter.
Kulob din Pillars da na Ikorodu United sun fafata ne a gasar firimiya ta kasa.

Boko Haram sun ƙone makarantu a Borno

Har yanzu ’yan bindiga ba su saki matar Manjo Janar Rabe ba

An binne gawar Manjo Janar Rabe a Katsina

Wasu tsiraru ne ke rura matsalar tsaro a Najeriya — Christopher Musa