Jami’in diflomasiyyar Italiya ya tsallake harin bam a Libiya

Wani jami’in dipflomasiyyar kasar Italiya da ya je cefane a Gundumar Zawiet Al-Dahmani da ke yankin birnin Tripoli, ya tsallake rijiya da baya, bayan da ya fice daga motarsa da aka dana mata bam, kafin bam din ya tashi.“Jami’in diplomasiyyar ya fice daga motarsa ne a gundumar Zawiet Al-Dahmani domin yin sayayya, sai kawai ya […]

Jami’in diflomasiyyar Italiya ya tsallake harin bam a Libiya
Jami’in diflomasiyyar Italiya ya tsallake harin bam a Libiya

Wani jami’in dipflomasiyyar kasar Italiya da ya je cefane a Gundumar Zawiet Al-Dahmani da ke yankin birnin Tripoli, ya tsallake rijiya da baya, bayan da ya fice daga motarsa da aka dana mata bam, kafin bam din ya tashi.
“Jami’in diplomasiyyar ya fice daga motarsa ne a gundumar Zawiet Al-Dahmani domin yin sayayya, sai kawai ya ga wata waya na reto a karkashin motarsa,” inji wani jami’in diflomasiyya. Direban motar ya kirawo ’yan sanda wadanda suka yi hanzarin killace wurin kafin bam din ya tashi. “An kawar da mutane daga wurin daga bisani cikin rabin sa’a motar ta tarwatse,” inji jami’in diflomasiyyar, wanda ya bukaci a sakaya sunansa.
A wata Janairun bana ne, karamin Jakadan Italiya da ke birni na biyu mafi girma a kasar Libiya wato Benghazi, Mista Guido De Sanctis ya sha da kyar a wani harin kisan gilla da aka kai masa a daidai lokacin da aka harbi motarsa mai sulke.
kasar Italiya ce ta yi wa Libiya mulkin mallaka, don haka suke da kyakkyawar dangantaka a zamanin marigayi Kanar Mu’ammar Gadhaffi, duk da cewa kasar ta shiga cikin Rundunar NATO da ta yake shi. Kuma a Benghazi aka fara yunkurion juyin juya-halin kawar da Gaddafi. Yawan hare-haren da ake ta kai wa wadanda suka rike mukami a zamanin Gaddafi na ta karuwa a wannan birni. Kuma birnin ya zama cibiyar masu fafutikar jihadi, har ma da wadanda suka kai harin kisan da aka yi wa Jakadan Amurka Chris Steben da wasu Amurkawa uku a ranar 11 ga Satumbar bara.