Jami’in DSS ya soka wa tsoho wuka kan N3,000

Jami’in DSS ya ki biyan kuɗin wuta sannan ya caka wa kiya-tekan gidan haya wuka

Jami’in DSS ya soka wa tsoho wuka kan N3,000

Jami’in hukumar DSS

Ana zargin wani jami’in hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) ya soka wa wani dattijo mai shekara 62 wuka kan Naira 3,000.

Shaidu sun bayyana cewa jami’in na DSS ya soka wa mutumin wuka a kwankwaso ne saboda taƙaddamar da suka yi kan kuɗin wutar lantarki Naira 3,000.

Dattijon mai suna Omoshola Oludele, shi ne kiya-tekan gidan da jami’in da DSS ke zaman haya a unguwar Tinumola da ke garin Osogbo, Jihar Osun.

Shaidu sun ce kiya-tekan ya je tattara kuɗin wutan gidan ne, amma jami’in ya ki biya, lamarin da ya kai su ga cacar baki, har jami’in ya caka masa wuka.

Wani ganau mai suna Tosin Moronkola, ya ce jami’in na DSS ya yi wa Mista Oludele mummunan rauni a kwankwaso, kuma an asibiti domin yi masa magani.

Mazauna unguwar sun bukaci ’yan sanda da sauran hukumomin da ke da alhaki su ɗauki mataki a kan jami’in na DSS domin guje wa aukuwar irin haka a nan gaba.

Wani babban jami’in DSS ya shaida wa wakilinmu cewa hukumar za ta bincika lamarin kuma za ta hukunta wanda ake zargin idan ta same shi da laifi.

Tags