Jami’in Hukumar SSS ya harbe wata mata a Kaduna
A shekaranjiya Laraba ce wata mata ta rasa ranta sakamakon harbin ta da jami’an tsaron cikin gida (SSS) suka yi a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja. Matar wadda ba a san wace ce ba ta rasu bayan harsashi ya same ta tana cikin motar haya a kan hanyarta ta dawowa daga Abuja tare da ’ya’yanta […]
A shekaranjiya Laraba ce wata mata ta rasa ranta sakamakon harbin ta da jami’an tsaron cikin gida (SSS) suka yi a kan hanyar Kaduna zuwa Abuja. Matar wadda ba a san wace ce ba ta rasu bayan harsashi ya same ta tana cikin motar haya a kan hanyarta ta dawowa daga Abuja tare da ’ya’yanta biyar.
Lamarin ya auku ne a kusa da garin Jere inda daga bisani aka ce an kai gawarta tsohon wurin karbar harajin motoci (Tall Gate) kusa da Sabon Gayan da misalin karfe 2:15 na rana.
Wata majiya ta ce ga alama jami’an ba matar suke hari ba, sun kuskure ne suka same ta da harsashin.
“Ba mu san abin da ke faruwa ba illa dai mun ga ’yan SSS sun iso kusa da inda muke cikin motocinsu biyu dauke da bindigogi. Can sai wata mota ta zo ta wuce, suka nemi direbar motar ya tsaya, da ya ki sai suka yi harbi da bindiga amma ba su samu direban ba wanda shi kadai ne a cikin motarsa. Tsautsayi ya sa harsashin ya samu matar wadda take dawowa tare da ’ya’yanta biyar cikin wata motar haya ta daga Abuja. Wannan abu ya tayar wa mutanen da ke wurin hankali har ya sa direbobin kananan motocin haya suka rufe hanyar Abuja zuwa Kaduna don nuna rashin jin dadinsu a kan a bin da ya faru,” inji wani da bai so a ambaci sunansa.
Aminiya ta samu labarin sai da Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kaduna, Adamu Ibrahim ya ziyarci wurin da abin ya faru domin bai wa direbobin hakuri tare da ba da umarnin a tsare jami’in SSS din da ya yi harbin. Kwamishinan ya ce tuni sun fara bincike kan hakikanin abin da ya faru.