Jami’in kasuwancinmu na Legas ya zama gwarzon wata

Jami’in kasuwanci na jaridar Aminiya da ke Jihar Legas, Tanimu Ahmed da sauran ma’aikatan Kamfanin Media Trust 10 sun lashe kyautar gwarzon watan Janairu da kamfanin ya sanya. Kamfanin Media Trust da ke buga jaridun Daily Trust da Weekly Trust da Sunday Trust da Aminiya da mujallar Kilimanjaro ya bai wa ma’aikatansa 11 da suka […]

Jami’in kasuwancinmu na Legas ya zama gwarzon wata
Jami’in kasuwancinmu na Legas ya zama gwarzon wata

Jami’in kasuwanci na jaridar Aminiya da ke Jihar Legas, Tanimu Ahmed da sauran ma’aikatan Kamfanin Media Trust 10 sun lashe kyautar gwarzon watan Janairu da kamfanin ya sanya.

Kamfanin Media Trust da ke buga jaridun Daily Trust da Weekly Trust da Sunday Trust da Aminiya da mujallar Kilimanjaro ya bai wa ma’aikatansa 11 da suka yi fice kyaututtuka daban-daban.
Bikin karramawar an yi shi ne a harabar kamfanin da ke Utako a Abuja inda ya samu halartar shugaban kamfanin Malam Kabiru Yusuf da babban Edita Mannir dan Ali da babban jami’in gudanarwa Abhay Desai da sauran manyan jami’an kamfanin da sauran ma’aikata.
Ma’aikatan da suka samu kyaututtukan sun hada da Tanimu Ahmed na sashen kasuwancin Aminiya da ke jihar Legas sai Amina Alhasan ta Weekly Trust da Aminu Nasidi na sashen talla na Abuja da Kamaluddeen Ayanbiyi na sashen mulki da gudanarwa.
Sauran sun hada da Abdulrasheed Ade Musa na sashen buga jaridu da Micheal Lassan na sashen sadarwa da Abdilhafeez Shittabey na sashen binciken kudi da Lucy Ogenyi ta sashen kasuwanci da Nilesh Nipane ta ofishin Kano da Hope Abbah ta ofishin Jos da kuma Shehu K. Goro na ofishin Kaduna.
A tattaunawarsa da Aminiya, jami’in sashen kasuwanci na Aminiya na jihar Legas ya bayyana farin cikinsa da zabensa da kamfanin ya yi.
Babban jami’in gudanarwa na kamfanin Abhay Desai ya bayyana cewa kamfanin ya bullo da kyautar ne don karfafawa ma’aikata gwiwar yin aiki tukuru bisa gaskiya da rikon amana.