Jami’in kudi na kamfanin MTN zai yi murabus

Babban Jami’in Kula da Harkokin Kudi na kamfanin MTN Mista Brett Goschen ya ce zai sauka daga mukaminsa.Ya ce zai yi hakan ne a karshen watan Satumba bana, kamar yadda ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.Mista Goschen ya kasance jami’in da ke kula da harkokin kudi na kamfanin daga watan Agustan […]

Jami’in kudi na kamfanin MTN zai yi murabus
Jami’in kudi na kamfanin MTN zai yi murabus

Babban Jami’in Kula da Harkokin Kudi na kamfanin MTN Mista Brett Goschen ya ce zai sauka daga mukaminsa.
Ya ce zai yi hakan ne a karshen watan Satumba bana, kamar yadda ya bayyana a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
Mista Goschen ya kasance jami’in da ke kula da harkokin kudi na kamfanin daga watan Agustan shekarar 2013. Gabanin haka ya taba zama Babban jami’in Zartarwa na Kamfanin a kasar nan. Har ila yau, jami’in ya kasance a kamfanin na tsawon shekara  14.
Sai dai kamfanin ya ce Mista Gunter Engling ne zai maye gurbin Mista Goschen a matsayin mukaddashin jami’in da zai kula da kudi.  Kuma shi ne tsohon Babban Jami’in Zartarwa na Kamfanin MTN reshen kasar Ruwanda. Har ila yau, ya rike mukamai da dama a kamfanin.