Jami’in Kwastam ya kashe kansa a Kano
Iyalan marigayin mai mukamin CSC ne suka sanar cewa ya harbi kansa da bindigarsa a gida
Wani jami’in hukumar kwastam ta Najeriya da ke aiki a Abuja ya harbe kansa har lahira a gidansa.
Jami’in mai suna Abdulwahab Magaji ya harbi kansa ne da bindiga kirar Pump Action ne a cikin bandaki a gidansa da ke Jihar Kano.
Iyalan marigayin mai mukamin CSC da ke aiki a Abuja ne dai suka sanar da ’yan sanda cewa ya harbi kansa da bindigarsa a gida.
Bayan isowar ’yan sanda ne aka dauke shi jina-jina zuwa asibiti inda likita ya sanar da su cewa rai ya yi halinsa.
Punch ta ruwaito cewa an sallama gawar ga iyalan mamacin domin yi mata jana’iza bisa tsarin Musulunci.
Kakakin hukumar kwastam na kasa, Abdullahi Maiwada, ya tabbatar da faruwar lamarin a gidan jami’in da ke Kano.
Wani abokin marigayin, mai suna Lawan Al-Amin Mohammed, ya tabbatar da rasuwar CSC Magaji, wanda ya bayyana a matsayin jajirtacce, mutumin kirki mai rikon amana kuma mai taimakon jama’a a lokacin rayuwarsa.