Jami’in Kwastam ya mutu yayin zaman kwamitin majalisa

Jami’in ya yanke jiki ya faɗi ana tsaka da zaman kwamitin majalisar wakilai a ranar Talata.

Jami’in Kwastam ya mutu yayin zaman kwamitin majalisa

Mataimakin Kwanturola a Hukumar Hana Fasa Ƙwauri ta Ƙasa, (Kwastam), Essien Etop Andrewya, ya yanke jiki ya mutu ana tsaka da zaman Majalisar Wakilai.

Ya zuwa yanzu babu wani cikakken bayan game da musababbin sanadin mutuwarsa ba.

Kakakin majalisar, Akin Rotimi Jr ne, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata sanarwa da ya fitar.

“Cikin tsananin baƙin ciki da nadama muna tabbatar da rasuwar wani babban jami’in hukumar kwastam ta Najeriya wanda ya kasance a zauren majalisar dokokin ƙasa domin ganawa da kwamitin majalisa.

“Yayin ganawar da jami’in da misalin ƙarfe 1 na ranar Talata, 25 ga Yuni, 2024, da alamar jami’in ba shi da rashin lafiya.

“Duk da ƙoƙarin gaggawa da ma’aikatan jinya na gaggawa da ma’aikatan lafiya na asibitin Majalisar Dokokin ƙasa suka ba shi, abin takaici ya rasu.

“Majalisar Wakilai ta miƙa saƙon ta’aziyyarta ga ’yan uwa da abokan arziƙin marigayin a cikin wannan mawuyacin lokaci.

“Mun san irin gagarumar gudunmawar da ya bayar ga hukumar Kwastam da kuma ƙasarmu.”

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda

An saki matar Ekweremadu daga gidan yari a Birtaniya, ta dawo Najeriya