Jami’in Sibil Difens ya mayar da N800,000 da wata Hajiya ta zubar a Adamawa
Jami’in ya nuna gaskiya tare dawo wa matar kuɗinta da suka ɓata.
Wani jami’in Hukumar Sibil Difens, Abubakar Abdulkadir Mayos, ya mayar da kuɗin wata maniyyaciya Naira 822,038 da suka ɓata a sansanin alhazai na Yola da ke Jihar Adamawa.
Kuɗin da aka samu sun haɗa da dala $505 da Riyal 30 na ƙasar Saudiyya, wanda ya kai kimanin Naira 822,038.
- An kama ƙasurgumin ɗan bindiga yayin tantance alhazai a Abuja
- Abba ya dakatar da hadiminsa saboda furta kalamai a kan Kwankwaso
Kuɗin mallakin Maimuna Salihu, wata maniyyaciya daga Jihar Taraba da ke shirin zuwa aikin Hajjin bana.
Jami’in ya mayar mata da kuɗin a ranar Lahadi, 18 ga watan Mayu, 2025.
An gudanar da bikin miƙa kuɗin a gaban jami’an Hukumar Alhazai ta Ƙasa (NAHCON), ciki har da jami’in Taraba, Daraktan Tsare-tsare, da wasu manyan jami’ai.