Jami’in tsaro na farin kaya ya harbe wani dan sanda
Ranar Talata a Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa, wani jami’in tsaro na farin kaya (NSCDC) ya dirke wani abokin aikinsa dan sandan kwantar da tarzoma (MOPOL) har lahira yayin da ’yan sandan na hadin gwiwa suke faman artabu da wasu ’yan fashi da makami a wata unguwa mai suna Etegwe. Dukkan jami’an tsaron na aiki […]
Ranar Talata a Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa, wani jami’in tsaro na farin kaya (NSCDC) ya dirke wani abokin aikinsa dan sandan kwantar da tarzoma (MOPOL) har lahira yayin da ’yan sandan na hadin gwiwa suke faman artabu da wasu ’yan fashi da makami a wata unguwa mai suna Etegwe.
Dukkan jami’an tsaron na aiki ne a rundunar ’yan sandan jihar, karkashin rundunar yaki da masu aikata miyagun halaye da aka yi wa lakabi da “Operation Doo Akpoo”, kamar yadda aka tabbatar wa Aminiya.
Majiyar ta nunin cewa, “Suna ta famar musayar wuta tsakaninsu da barayin ne, bisa tsautsayi, kokarin da shi dan sandan kwantar da tarzoman yake yi na ya shawo kan barayin yana harbinsu hakan ta kasance.”
Wakilinmu ya tuntubi Mista Aled Akhigbe, jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan, wanda ya gaskata faruwar lamarin kuma ya ce “kaddara ce, wadda ta riga fata”.