Jami’in yakin neman zaben Buhari, Danladi Pasali, ya rasu

Marigayin shi ne shugaban kungiyar Buhari Campaign Organisation (BCO).

Jami’in yakin neman zaben Buhari, Danladi Pasali, ya rasu

Marigayi Alhaji Danladi Pasali tare da Shugaba Buhari

Jami’in kungiyar yakin neman zaben Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wato Buhari Campaign Organisation (BCO), Alhaji Danladi Pasali, ya rasu.

Ya rasu ne a wani asibiti da ke Babban Birnin Tarayya Abuja ranar Talata.

Aliyu Pasali, wani kane ga mamacin, shi ne ya tabbatar da rasuwar dan uwan nasa a Jos, babban birnin Jihar Filato.

Shekara biyu da suka gabata, sunan marigarin ya yi tambari lokacin da ya bukaci a gaggauta kama masu shirya zanga-zangar #RevolutionNow, yana mai cewa ’yan Najeriya yanzu sun yi wayewar da wani ba zai zo yana yi wa hadin kan kasa zagon kasa ba.

Pasali ya ce duk wani yunkuri na tunzura jama’a su nemi canjin gwamnatin dimokuradiyya ba ta hanyar zabe ba daidai yake da cin amanar kasa, kuma haka ya kamata jami’an tsaro su dauke shi.

Ya ce Kundin Tsarin Mulkin Najeriya ya yi bayanin yadda za a iya sauya gwamnati a tsarin dimokuradiyya.