Jamilu Collins zai yi jinya zuwa karshen kakar wasanni ta bana

Jamilu ya buga wa Najeriya kwallo a gasar Cin Kofin Afirka a watan Janairu.

Jamilu Collins zai yi jinya zuwa karshen kakar wasanni ta bana

Jamilu Collins

Dan wasan baya na tawagar Najeriya da kungiyar kwallon kafa ta Cardiff City, Jamilu Collins, zai yi doguwar jinya sakamakon rauni da ya samu a gwiwa.

Jamilu wanda rahotanni ke cewa ya kara wa Cardiff City farin jini, ya gurde ne a gwiwa a karawarsu da West Bromwich Albion wanda aka tashi canjaras babu ci.

Ana sa ran za a yi wa Jamilu aiki a gwiwar tasa cikin ‘yan makonnin masu zuwa, wanda zai shafe tsawon lokaci yana jinya har zuwa kakan wasanni ta badi mai zuwa.

Tuni abokan wasansa a kungiyar ta Cardiff suka soma kewarsa, inda kocin kungiyar, Steve Morrison ke tausaya wa dan wasan laakari da cewa ba zai sake taka leda ba sai a kaka wasanni mai zuwa.

Morrison ya kuma yaba wa kwazon Jamilu, wanda aka bayyana a matsayin dan wasan baya mafi kwarewa a gasar Ingila ajin ’yan dagaji wato Championship.

Ana iya tuna cewa, Morrison ne ya dauko Jamilu daga kungiyar 3 Liga mai buga gasar Bundesliga aji ’yan dagaji na uku a lokacin bazarar da ta wuce.

Kafin nan, Jamilu ya buga wa Najeriya kwallo a gasar Cin Kofin Afirka a watan Janairu tare da Alex Iwobi da kuma Kelechi Iheanacho.