Jami’o’i 8 da gwamnati ta amince ’yan Nijeriya su yi karatun digiri a Benin da Togo

Waɗancan “haramtattun” cibiyoyin ilimi suna zubar da mutuncin Nijeriya.

Jami’o’i 8 da gwamnati ta amince ’yan Nijeriya su yi karatun digiri a Benin da Togo

Universite de Lome

Gwamnatin Tarayya ta ce jami’o’i takwas ne kacal ta amince ’yan Nijeriya su yi karatun digiri a ƙasashen Benin da Togo.

Ministan Ilimi Farfesa Tahir Mamman ya bayyana haka a ranar Lahadin da ta gabata.

Ya kuma ce babu gudu babu ja da baya kan shawarar da gwamnatin ta yanke na soke shaidar digiri dubu 22 da 700 da wasu “jabun” jami’o’i a Benin da Togo suka ba ’yan Nijeriya.

Ministan wanda yake magana a shirin Sunday Politics na gidan talabijin na Channels, ya ce shawarar soke digirorin ba ta yi tsauri ba, ganin ’yan Nijeriya da suka samu digiri daga waɗancan “haramtattun” cibiyoyin ilimi suna zubar da mutuncin ƙasar nan ne, sannan hukumomi a ƙasashen na rainon Faransa sun tabbatar da cewa waɗancan makarantu na jabu ne.

Idan za a iya tunawa a ranar Juma’ar da ta gabata ce ne a wajen taron cika shekara ɗaya a kan muƙaminsa Ministan ya bayyana wa manema labarai cewa za a soke takardun digiri na ’yan Nijeriya sama da dubu 22 da 700 da suka yi a jabun makarantun ƙasashen biyu

Ministan ya ce, wannan mataki wani ɓangare ne na rahoton da aka miƙa wa Majalisar Zartarwa ta Kasa da kwamitin da aka ba aikin bincikar almundahanar bayar da digiri a jami’o’in Nijeriya da ƙasashen waje, sakamakon wani rahoton fallasa da wani ɗan jaridar Nijeriya ya yi wanda ya samu digiri daga wata jami’a a Jamhuriyar Benin a ƙasa da wata biyu, kuma ya yi amfani da shi aka tura shi hidimar ƙasa.

Ministan ya ce gwamnati ta amince da jami’o’i uku ne kacal a Togo sai biyar a Benin, inda ta bayyana sauran a matsayin haramtattu.

Jami’o’in da gwamnatin ta amince ’yan Nijeriya su je su yi karatun digiri a ciki a Togo sun haɗa da:

  1. Universite de Lome
  2. Universite de Kara
  3. Catholic University of West Africa.

Sai na Jamhuriyyar Benin:

  1. Universite d’Abomey­ Calavi
  2. Universite de Parakou
  3. Universite Nationale des Sciences, Technologies Ingenierie Et Mathematiques.
  4. Universite Nationale d’Agriculture.
  5. Universite Africaine de Deɓelopment Cooperatif.