Jami’o’in Birtaniya za su fara daukar masu sakamakon jarabawar NECO

Jami’o’in kasar Birtaniya na shirin fara daukar daliban Najeriya masu shaidar jarabawar kammala sakandare ta NECO. Shugaban hukumar shirya jarabawa ta kasa (NECO), Farfesa Ibrahim Wushishi, ya ce Jami’ar Lead da Jami’ar Birmingham City da ke kasar Birtaniya sun tuntubi hukumar  kan jarabawar da take shiryawa. Ya ce  jami’o’in sun fara tunanin bai wa daliban […]

Jami’o’in Birtaniya za su fara daukar masu sakamakon jarabawar NECO

Jami’o’in kasar Birtaniya na shirin fara daukar daliban Najeriya masu shaidar jarabawar kammala sakandare ta NECO.

Shugaban hukumar shirya jarabawa ta kasa (NECO), Farfesa Ibrahim Wushishi, ya ce Jami’ar Lead da Jami’ar Birmingham City da ke kasar Birtaniya sun tuntubi hukumar  kan jarabawar da take shiryawa.

Ya ce  jami’o’in sun fara tunanin bai wa daliban Najeriya gurbin karatu da sakamakon jarabawarsu ta NECO.

A fahimtarsa, hakan na nuni da  amincewa da ingancin sakamakon jarabawar NECO ne a idanun manyan jami’o’in ciki da wajen Najeriya.

Farfesa Wushishi ya bayyana hakan ne yayin wani taron tattaunawa da ’yan jarida a Abuja ranar Laraba.

Ya ce NECO ta cika sharudan Jami’ar Birmingham City, kuma a halin yanzu suna aiki tukuru kan ganin sun sami cika sharudan jami’ar Lead.

Ya tona kabarin mijin mahaifiyarsa ya yanke kansa a Adamawa

Zaftarewar ƙasa ta kashe mata masu haƙar zinare a Mali

Matashi ya yi lalata da ’yan firamare biyu a Zariya

Shekara 18 aikin Asibitin Sabuwar Kaduna na tafiyar hawainiya