Jam’iyyar Accord ta kori shugabanninta kwana 2 kafin zaben gwamna
Malam Muhammad Nalado ya kuma karyata ikirarin tsohon shugaban jam’iyyar da ke cewa uwar jam’iyyar ta kulla yarjejeniyar goyon bayan Gwamna Makinde a zaben da ke tafe.
Jam’iyyar Accord ta sallami shugabanninta na Jihar Oyo kwana biyu kafin zaben gwamna da ke tafe.
Uwar jam’iyyar ta kore su ne bayan shugabannin jam’iyyar na Jihar sun bayyana goyon bayansu ga Gwamna Seyi Makinde na Jam’iyyar PDP, a zaben gwamna da ke tafe ranar Asabar.
- Tirela makare da kankana ta yi hatsari a Jigawa
- ’Yan sanda sun kashe dan bindiga sun cafke wani a Katsina
Ta kuma fitar da jerin sunayen sabbin shugabanninta a jihar bayan da Shugban Jam’iyyar na Kasa, Muhammad Nalado ya gudanar da taron manema labarai inda ta la’anci abin da jagorancin jam’iyyar a Jihar Oyo karkashin Kolade Ojo ya yi.
Malam Muhammad Nalado ya kuma karyata ikirarin tsohon shugaban jam’iyyar da ke cewa uwar jam’iyyar ta kulla yarjejeniyar goyon bayan Gwamna Makinde a zaben da ke tafe.