‘Jam’iyyar AD za ta kafa gwamnati a shekarar 2019’
Shugaban Jam’iyyar AD reshen Jihar Bauchi Alhaji Mahmood Mairiga ya ce jam’iyyar za ta iya kafa gwamnati a matakin tarayya da jihohi a zaben 2019, idan aka lura da yadda take dada farfadowa a yanzu.Alhaji Mairiga ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a Bauchi, dangane da inda jam’iyyar ta kwana […]
Shugaban Jam’iyyar AD reshen Jihar Bauchi Alhaji Mahmood Mairiga ya ce jam’iyyar za ta iya kafa gwamnati a matakin tarayya da jihohi a zaben 2019, idan aka lura da yadda take dada farfadowa a yanzu.
Alhaji Mairiga ya bayyana haka ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a Bauchi, dangane da inda jam’iyyar ta kwana bayan kammala zaben bana.
Ya ce duk da cewa a zaben da aka gudanar watannin baya Jam’iyyar AD ce ta hudu a samun dimbin kuri’u don haka suna da yakinin za ta iya komawa sahun gaba kafin zabe mai zuwa.
Shugaban ya ce a dukkan kananan hukumomin jihar 20 akwai shugabannin jam’iyyar kuma yana tabbatar wa al’umma cewa ko gobe aka shirya zaben kananan hukumomi a Jihar Bauchi, Jam’iyyar AD za ta lashe mafi yawan kujerun kananan hukumomin.
Alhaji Mairiga ya ce ya shiga Jam’iyyar AD ne tun a 1999 domin ya gamsu da manufofinta, inda ya yi kira ga shugabannin jam’iyyar a matakin kasa su kai mata dauki a jihar, “Domin duk shekara ni nake biyan sama da Naira dubu 150 wajen biyan kudin hayar ofishinta a jihar.
Sai ya yi kira ga Shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnoni da ’yan majalisa su ba da fifiko wajen cika alkawuran da suka dauka a lokacin kamfe.