Jam’iyyar adawa ta kama hanyar lashe zabe a Indiya

Wani hasashen masana ya bayyana cewa jam’iyyar adawa ta Bharatiya Janata Party (BJP) wadda Mista Narendra Modi ke jagoranta ta kama hanyar samun nasara a zaben kasar Indiya, wanda aka kammala a ranar Litinin.An dai raba zaben ne har zango tara, wanda jama’ar da suka cancanci kada kuri’ia fiye da miliyan dari 5 ne suka […]

Jam’iyyar adawa ta kama hanyar lashe zabe a Indiya
Jam’iyyar adawa ta kama hanyar lashe zabe a Indiya

Narendra Modi na Jam’iyyar Bharatiya JanataWani hasashen masana ya bayyana cewa jam’iyyar adawa ta Bharatiya Janata Party (BJP) wadda Mista Narendra Modi ke jagoranta ta kama hanyar samun nasara a zaben kasar Indiya, wanda aka kammala a ranar Litinin.
An dai raba zaben ne har zango tara, wanda jama’ar da suka cancanci kada kuri’ia fiye da miliyan dari 5 ne suka ziyarci dubun-dubatan rumfunar zabe da ke kasar. Hakan ya sa zaben ya zama mafi girma a duniya. Masana dai sun yi hasashen cewa fafatawa za tai zafi ne a tsakanin jam’iyya mai mulki, Congress Party da kuma jam’iyyar BJP.
Ranar Litinin da ta gabata ne aka rufe dukkanin rumfunan zabe, bayan kwashe fiye da wata guda ana kada kuri’u. Yau Juma’a ne za a fara kidaya kuri’un a hukumance.’Yan takara 42 ne suka fafata don neman zama Firaminista, ciki har da na jam’iyya mai mulki, Ajay Rai.
Kowace a cikin  jam’iyyun dai na bukatar lashe kujerun majalisa 272 ne kafin ta iya kafa gwamnati a kasar.Jam’iyyar adawa ta BJP na kan hanyar samun wannan adadin. Idan kuma ta kasa, to bayan kammala kidaya kuri’un a yau (Juma’a) za ta nemi hadakar wasu kananan jam’iyyu don su tallafa da goyon baya.