Jami’yyar adawa ta karɓe mulki bayan shekaru 14 a Birtaniya
Fira Minista Rishi Sunak, ya amsa shan kayi bayan shekaru 14 Jam’iyyarsa na mulki a Birtaniya
Jami’yyar adawa ta Labour ta kawo karshen shekara 14 na mulkin Jam’iyyar Conservative a kasar Birtaniya.
Kazalika Labour ta kwace kujerar tsohuwar fira ministar Birtaniya Liz Truss da ke wakiltar mazabar Norfolk ta Kudu maso Yamma a Majalisar Dokokin kasar.
Jam’iyyar Labour ta kafa tarihin doke Conservative ne bayan zaben ranar 5 ga watan Yuli inda ta samu rinjayen kujeru a majalisar dokokin kasar.
A yayin da zaben ke ci gaba da kirga kuri’u, Fira Minista Rishi Sunak, ya amsa shan kayi.
Ya sanar da cewa, “na dauki laifin wannan faduwa da muka yi.”
Da wannan shan kaye, Rishi Sunak zai sauka daga kujerar Fira Ministan, wadda Shugaban Jam’iyyar Labour, Keir Starmer, zai dare domin kafa sabuwar gwamnati.
Da yake jawabi, Starmer ya ce, “yau mun bude wani sabon babi a Birtaniya.”
Ya ci gaba da cewa, “nasarar zabe ba daga sama take fadowa ba, sai da yaki da gwagwarmaya.
“Shi ya sa a wannan karo Jam’iyyar Labour ta kai ga narasa.”