Jam`iyyar adawa ta SDP ta taya Buhari murnar lashe zabe
Mukaddashshin shugaban jam’iyyar adawa ta (SDP), Farfesa Tunde Adeniran, ya taya Shugaba Buhari murnar lashe zabensa karo na biyu kuma ya bukace shi da ya yi amfani da wannan damar wajen inganta hadin kan ‘yan Najeriya da tabbatar da zaman lafiya a kasar. Farfesa Tunde ya bayyana hakan ne a wasikar da ya aikawa shugaban. […]
Mukaddashshin shugaban jam’iyyar adawa ta (SDP), Farfesa Tunde Adeniran, ya taya Shugaba Buhari murnar lashe zabensa karo na biyu kuma ya bukace shi da ya yi amfani da wannan damar wajen inganta hadin kan ‘yan Najeriya da tabbatar da zaman lafiya a kasar.
Farfesa Tunde ya bayyana hakan ne a wasikar da ya aikawa shugaban. Kamar yadda Daraktan watsa labarai na jam’iyyar SDP Yemi Akinbode ya bayyanawa manema labarai.