Jami’yyar ADP ta sa zare da dan takararta na Gwamna
Jam’iyyar Action Democratic Party (ADP) ta nesanta kanta da matakin da dan takararta na Gwamna a Jihar Oyo Cif Christopher Alao Akala ya dauka na mara wa dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar baya. A wata sanarwa dauke da sa hannun Babban Sakataren Jam’iyyar ta Kasa Dokta Stebe Uwazie da aka […]
Jam’iyyar Action Democratic Party (ADP) ta nesanta kanta da matakin da dan takararta na Gwamna a Jihar Oyo Cif Christopher Alao Akala ya dauka na mara wa dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar baya.
A wata sanarwa dauke da sa hannun Babban Sakataren Jam’iyyar ta Kasa Dokta Stebe Uwazie da aka raba wa manema manema labarai da jam’iyyar ta ta gudanar a shekaranjiya Laraba, Jam’iyyar ADP ta ce dan takararta na Shugaban Kasa Injiniya Yabagi Yusuf Sani bai janye daga neman kujerar ba, saboda haka ta shawarci magoya bayanta su yi watsi da bayanin Alao Akala.
Sakataren ya ce Cif Akala wanda ya bayyana mara wa Atiku baya yayin tsokaci da ya yi a jaridar Banguard ta ranar Lahadi 17 ga Fabrairu kan batun dage ranar zabe zuwa gobe Asabar, inda ya shawarci magoya bayansa su zabi Atiku maimakon dan takararta Injiniya Yusuf Yabagi, ta gargadi dan takarar Gwamnan ya janye furucin ko ya fuskanci matakin ladabtarwa daga shugabannin jam’iyyar na kasa.
“Jamiyyar ADP na ganin matakin a matsayin ungulu da kan zabo da ba za ta amince da shi ba, kuma babu wani lokaci da muka zauna muka dauki matakin yin hadin gwiwa da wata jam’iyya,” inji sanarwar.